Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Mai ba gwamnan Jihar Katsina shawara kan ayyukan ƙananan hukumomi, Hon. Lawal Rufa’i Safana, ya bayar da umarnin soke kwangilar aikin gina gidajen .alaman asibitocin mataki na farko (PHCs) da ake gudanarwa a ƙananan hukumomin Funtua da Sabuwa, dalilin rashin bada himma ga aikin kwangilar da nuna ko in kula ga aiki da ɗan kwangilar ke nunawa bayan ya karɓi kuɗin somin taɓi tun ƙarshen shekarar 2025.
Haka kuma ya bai wa ɗan kwangilar da ke gudanar da irin wannan aiki a ƙaramar hukumar Dandume wa’adin sati biyu kacal da ya kammala aikin tare da gyara duk wata matsala da aka lura da ita. Ya gargaɗe shi cewa idan ya gaza cika wannan wa’adi, gwamnati za ta soke kwangilar tare da ƙwace aikin daga hannunsa.
Wannan mataki ya biyo bayan wata ziyarar ba zata da ya kai da karɓar rahoton injiniyoyin sa akan ayyukan. Ya yi umarnin ƙananan hukumomin su gaggauta kawo masa lissafin iyakar aikin da ɗan kwangilar ya yi domin biyan sauran abunda aka biyo shi, kuma a nemi wasu yan kwangila na gari don ayi yarjejeniyar kammala aikin da su.
Daga ƙarshe, yayi kira ga ‘yan kwangilar dake ayyuka a ƙananan hukumomi su maida hankali su rinƙa yin kyawawan ayyuka daidai da tsarin da aka sa hannu tsakaninsu da ƙananan hukumomi domin ma’aikatar kula da ayyukan ƙananan hukumomi ba za ta sassauta matsayinta akan wannan ba.
Hon Safana ya jaddada cewa gwamnatin Jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin Malam Dikko Umaru Raɗɗa, ba za ta lamunci sakaci ko aiwatar da ayyukan da ba su kai matsayin ingancin da ake buƙata ba.
Ya ƙara da cewa duk wani ɗan kwangilar da ya gaza cika sharuɗɗan kwangila ko samar da ingantaccen aiki zai fuskanci matakin da ya dace, domin tabbatar da cewa al’ummar jihar suna amfana da ayyukan ci gaba masu inganci, ɗorewa da kuma ƙima ga kuɗaɗen jama’a.
