Daga IBRAHIM HAMISU a Kano
Ƙungiyar wakilan kafofin yaɗa labarai ta Kano (Kano Correspondents’ Chapel) ƙarƙashin ƙungiyar ‘yan jarida ta Najeriya (NUJ), ta bayyana cewa mambobinta sun amfana da tallafin walwala da kuma shirye-shiryen taimakon kuɗi a cikin shekara guda da ta gabata, yayin da shugabancin ƙungiyar ya gabatar da rahoton ayyukansa, wanda ya ƙunshi nasarorin da aka samu a fannin walwalar mambobi, bunƙasa ƙwarewar aikin jarida da kuma gyaran tsarin gudanarwa.
Shugaban ƙungiyar, Murtala Adewale, ne ya gabatar da rahoton a yayin taron gabatar da rahoton shekara ɗaya da kuma bikin cika shekara guda na shugabancinsa, wanda aka gudanar a sakatariyar NUJ da ke Kano.
Rahoton ya nuna cewa shugabancin ya bai wa walwalar mambobi muhimmanci, inda ya bayar da tallafin kai tsaye na naira dubu 500 ga mambobi 10, ya taimaka wajen samar da rancen kuɗi da ya kai naira miliyan 8.5, ya samar da guraben aikin Hajji guda biyu, ya taimaka da naira miliyan biyu domin kula da lafiyar wani mamba, tare da rabon kayan abinci na watan Ramadan da darajarsu ta kai naira miliyan 2.5.
Adewale ya kuma bayyana cewa kwamitin gudanarwar ya samar wa mambobi ƙarin tallafin musamman na naira dubu 30 a duk wata, lamarin da ya sanya jimillar kuɗaɗen tallafin kai tsaye da aka samar cikin shekara ta kai naira miliyan 9.5.
Baya ga walwala, rahoton ya nuna cewa shugabancin ya ƙaddamar da shirye-shirye daban-daban domin inganta ƙwarewar aikin jarida da bunƙasa alaƙa tsakanin mambobi.
Daga ciki akwai ƙaddamar da shirin Tea Break Platform domin ƙarfafa mu’amala da musayar ilimi, shirya taron horaswa na kwanaki huɗu a Kaduna tare da ɗaukar dukkanin kuɗaɗen mahalarta, da kuma ƙaddamar da lambar yabo ta Distinguished Awards of Excellence domin karrama tsofaffin shugabanni, gogaggun ƴan jarida da fitattun mambobin ƙungiyar.
Hakazalik, shugabancin ya kafa ƙungiyar haɗin gwiwa (Cooperative Society) mai jarin farko na naira miliyan 10 domin sauƙaƙa wa mambobi samun tallafin kuɗi, tare da gina filin wasan ƙwallon tebur na zamani (Olympic Standard Table Tennis) domin inganta nishaɗi da lafiyar ‘yan jarida.
A wani mataki na ƙara fito da ayyukan ƙungiyar fili, shugabancin ya wallafa Government Compendium, wani kundin da ya tattara muhimman nasarori da ayyukan ci gaban gwamnatin Jihar Kano.
Rahoton ya kuma bayyana wasu sauye-sauye da aka yi a ofishin ƙungiyar, ciki har da samar da intanet mai saurin 5G ba tare da iyaka ba, girka na’urar DSTV tare da ci gaba da biyan kuɗin amfani da ita, ɗaukar ma’aikacin tsafta domin kula da ofisoshi da banɗakuna, sayen tukunyar ruwa ta lantarki, sake kunna asusun bankin ƙungiyar domin ƙarfafa gaskiya da riƙon amana, buɗe shafin Facebook, da kuma ci gaba da samar da shayi, garin kwaki da sauran abubuwan shakatawa ga mambobi.
Da yake gabatar da rahoton, Adewale ya ce duk waɗannan nasarori sun samu ne sakamakon haɗin kai, goyon baya da jajircewar mambobin ƙungiyar. Ya ce shugabancin nasa zai ci gaba da tafiya bisa turbar gaskiya, riƙon amana da hidima ga mambobi.
Ya yi kira ga ƴan jarida da su ci gaba da haɗa kai domin kare martabar aikin jarida, yana mai jaddada cewa haɗin kai da fahimtar juna su ne ginshiƙan gina ƙungiya mai ƙarfi da ci gaba.
Shugaban ya ƙara da cewa shugabancin zai gina kan nasarorin da aka samu a shekara ta farko ta hanyar ƙaddamar da sabbin shirye-shirye da za su ƙara inganta walwalar mambobi, ƙarfafa ɗabi’un aikin jarida da kuma haɓaka ƙwarewar ‘yan jarida wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansu.
Taron gabatar da rahoton shekara ɗaya ya kasance wani ɓangare na bukukuwan cika shekara guda na shugabancin ƙungiyar, inda ya samu halartar manyan ‘yan jarida, shugabannin kafafen yaɗa labarai, malaman jami’a, wakilan gwamnati da na ƙungiyoyin ƙwararru, waɗanda suka yaba da matakin da ƙungiyar ta ɗauka na inganta gaskiya da riƙon amana ta hanyar gabatar da rahoton ayyukanta ga jama’a.
