Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamna Raɗɗa ya yaba da cancanta da ƙwarewa bayan wasu ‘yan asalin Katsina sun samu muƙamin kwamishinan ‘yan sanda.
Ya gode wa sufeto janar na ‘yan sanda, IGP Disu bisa amincewar da ya nuna ga jami’an Katsina, ya ce za su cigaba da bautawa Nijeriya cikin gaskiya da ƙwarewa.
Sabbin jami’an da aka ɗaga zuwa wannan babban muƙami sun haɗa da CP Nuhu Na Aliya Darma daga ƙaramar hukumar Rimi, CP Ibrahim Usman Lukunche daga ƙaramar hukumar Katsina, da kuma CP Tijjani Murtala Mohammed daga ƙaramar hukumar Safana.
CP Nuhu na Aliya Darma ya gina kyakkyawar sana’arsa a rundunar ‘yan sanda ta hanyar nuna ƙwarewa, biyayya ga doka da oda, tare da jagoranci nagari a fannoni daban-daban na gudanarwa da ayyukan tsaro.
CP Ibrahim Usman Lukunche gogaggen jami’in ɗan sanda ne da aka san shi da jajircewa wajen tabbatar da tsaron jama’a, ƙwarewa a aiki da kuma himma wajen wanzar da zaman lafiya da tsaro.
Haka kuma, CP Tijjani Murtala Mohammed ya yi fice a ayyuka daban-daban na rundunar ‘yan sanda, inda ya samu girmamawa saboda gaskiyarsa, ƙwarewarsa da sadaukarwarsa wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Gwamna Raɗɗa ya bayyana cewa wannan ƙarin girma wata babbar shaida ce ta ƙwarewarsu, cancantarsu, gaskiyarsu da kuma jajircewarsu wajen kare rayuka da dukiyoyin al’umma a faɗin ƙasar nan.
Ya ce, “wannan ƙarin girma da waɗannan fitattun jami’ai suka samu abin alfahari ne ga gwamnati da al’ummar Jihar Katsina.
“Hakan ya nuna irin amincewa da aka yi da jagorancinsu, gogewarsu da kuma kyakkyawan tarihin ayyukan da suka yi wa ƙasa.”Inji Dikko Raɗɗa.
Gwamnan ya ƙara da cewa nasarorin da waɗannan manyan jami’an suka samu za su zama abin koyi ga matasan Jihar Katsina wajen rungumar aikin gwamnati cikin sadaukarwa, ladabi da kishin ƙasa.
Ya ce, “Nasararsu ta tabbatar da cewa aiki tuƙuru, gaskiya da jajircewa wajen gudanar da aiki koyaushe suna samun lada. Ina taya su murna bisa wannan gagarumin ci gaba, tare da ƙarfafa musu gwiwa da su ci gaba da gudanar da aikinsu cikin adalci, ƙwarewa da mutunta doka.”Raɗɗa ya ce.
Gwamna Raɗɗa ya bayyana ƙwarin gwiwarsa cewa sabbin Kwamishinonin ‘yan sandan za su ci gaba da ba da gudunmawa wajen ƙarfafa tsaron ƙasa da tabbatar da zaman lafiya a faɗin Nijeriya.
Haka kuma, gwamnan ya miƙa godiyarsa ga Sufeto Janar na ‘yan sandan Nijeriya, IGP Olatunji Rilwan Disu, bisa amincewar da ya nuna ga waɗannan jami’an uku daga Jihar Katsina, yana mai bayyana tabbacin cewa za su ci gaba da yi wa ƙasa hidima cikin gaskiya, ƙwarewa da sadaukarwa.
A madadin gwamnati da al’ummar Jihar Katsina, Gwamna Raɗɗa ya yi wa sabbin kwamishinonin ‘yan sandan addu’ar Allah ya ba su nasara da shiriyar sa wajen gudanar da sabbin nauyin da aka ɗora musu.
