2027: Tikitin NDC na Obi da Kwankwaso ba zai yi nasara ba a Kano, inji Ganduje

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Tsohon shugaban jam’iyyar APC, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce tikitin takarar shugaban ƙasa da ya haɗa Peter Obi da Rabi’u Musa Kwankwaso a jam’iyyar NDC ba zai yi nasara ba a Jihar Kano a babban zaɓen 2027.

Ganduje, wanda kuma tsohon gwamnan jihar Kano ne, ya faɗi haka ne yayin ganawa da ‘yan jarida a ranar Talata, inda ya ce tikitin takarar ba shi da ƙarfi a siyasance, karɓuwa ko kuma tarihin shugabanci da ake buƙata domin samun goyon bayan al’umma a jihar.

“Ba na tunanin tikitin Peter Obi da Kwankwaso zai yi nasara a Kano. Ba zai yi nasara ba. In taƙaice muku, ya zama gawa tun kafin a kai lokacin,” inji shi.

Tsohon shugaban APCn ya ƙalubalanci tarihin rahoton da Obi ya kafa a lokacin da yake gwamnan Jihar Anambra, inda ya ce aikin da ya yi bai kai a ce ya samu ƙwarewar da zai shugabanci Nijeriya ba.

Haka kuma, Ganduje ya soki tarihin shugabancin Kwankwaso, wanda shi ma tsohon gwamnan Kano ne, yana mai cewa ya gaza samun wa’adin gwamna biyu a jere kamar sauran waɗanda suka yi gwamna a jihar.

A cewarsa, Kwankwaso bai yi aikin da ya cancanci zama mataimakin shugaban ƙasa ba da har zai gamsar da jama’a su zaɓe su ba, yana mai jaddada cewa tikitin NDC a zaɓen shugaban ƙasa na 2027 ba zai nasara ba.

By Babaji

Leave a Reply