Tinubu ya kafa sabuwar bataliyar sojoji a Kwara

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A ƙoƙarinsa na ƙarfafa tsaro da yaƙi da ‘yan bindiga, masu garkuwa da mutane da sauran miyagun laifuka, Shugaba Bola Ahmed Tinubu, ya amince da kafa sabuwar bataliyar sojoji a Jihar Kwara.

A sanarwar da Mataimakin Sakataren yaɗa labaran Gwamnan Kwara, Mashood Agboola ya fitar, gwamna AbdulRahman AbdulRazaq ya ce za a kafa bataliyar ne a garin Omu Aran, wato hedikwatar Ƙaramar Hukumar Irepodun.

Gwamna AbdulRazaq ya yaba wa Tinubu bisa amincewa da bukatar, yana mai cewa sabon sansanin sojojin zai kara karfin ayyukan yaki da ta’addanci da masu garkuwa da mutane a jihar.

Ya kuma yi godiya ga babban hafsan sojin kasa, Laftanar Janar Waidi Shaibu, da Ofishin Mai Bai Wa Shugaban Kasa Shawara Kan Tsaro da sauran hukumomin tsaro bisa hadin gwiwar da suke yi wajen magance matsalolin tsaro.

Wannan na zuwa ne yayin da ake cigaba da nuna damuwa kan taɓarɓarewar al’amuran tsaro a wasu sassan jihar, musamman a yankin al’ummar Babanla da ke Ƙaramar Hukumar Ifelodun, inda mazauna ke zargin ‘yan bindiga da cigaba da kai hare-hare.

By Babaji

Leave a Reply