
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Matatar Man Fetur ta Ɗangote ta koma sayar da fetur da kuɗin naira bayan dakatar da tsarin amfani da dala yayin da ta kuma yi ƙarin N140 daga yadda ta saba sayarwa a defo.
Hakan na zuwa ne bayan da matatar, mai samar da gangar mai 650,000 a kullum, ta dakatar da dakon fetur da koma wa amfani da dala wajen tsara farashi, lamarin da ya janyo tsaiko a harkar samarwa da kasuwar fetur da ya sa aka samu ƙarin farashi a defo.
Matatar ta yi wannan sanarwa ne a wani saƙon da ta wallafa shafin tsare-tsaren farashi na yanar gizo – Petroleumprice.ng.
Sanarwar ta nuna cewa ƙarin daga N1,075 na kowane zuwa N1,215 ya nuna cewa an ƙara N140 ko kuma kaso 13.02.
Haka kuma, ta ƙara farashin lodi daga defo akan N1,441,575 ga kowane tan, ya koma N1,602,495.
A cewar sanarwar, sabon tsarin farashin zai fara aiki ne a nan take, wato daga ranar 22 ga Yuli, 2026, tana mai kira ga masu saye da su tuntuɓe ta domin neman ƙarin bayani akan al’amarin.
