DSS ta ceto sauran ɗaliban Polytechnic huɗu da aka sace a Zamfara

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar Tsaro ta Farin kaya DSS a Jihar Zamfara, ta yi nasarar ceto sauran ɗalibai guda huɗu da aka yi garkuwa da su Ƙaramar Hukumar Ƙauran Namoda, ‘yan makarantar ‘Federal Polytechnic’ da ke ƙaramar hukumar.

Rahotanni sun bayyana cewa, jami’an sun samu wannan nasara ne bayan amfani da wasu bayanai na sirri, lamarin da ya ba su damar ceto ɗaliban da suka haɗa da maza uku da mace guda a ranar Laraba ba tare da biyan kuɗin fansa ba.

Haia kuma, an ruwaito cewa an kama ɗaya daga cikin masu garkuwar a lokacin atisayen ceton yayin da aka halaka sauran ‘yan bindigar.

A ranar 3 ga watan Yuni ne aka yi garkuwa da ɗaliban a gidajen wajen harabar makarantar da ke yankin Low-cost a garin Ƙauran Namoda bayan wasu ‘yan bindiga sun kai farmaki, inda suka yi awon-gaba da ɗalibai guda shida.

Bayan sako biyu daga cikinsu, jami’an tsaro sun cigaba da ƙoƙarin ganin sauran ɗaliban sun shaƙi iskar ‘yanci cikin aminci.

Hakan na zuwa ne bayan da jami’an hukumar suka yi nasarar ceto wani farfesa na na Jami’ar Jihar Nasarawa da ke Keffi, yayin da suka samu nasara a da dama daga cikin ire-iren atisayen a ‘yan kwanakin nan a sassan shiyyar Arewa maso Yamma.

By Babaji

Leave a Reply