Rundunar soji na neman wani jami’i ruwa a jallo kan samar wa ‘yan ta’adda kayan sojoji

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hedikwatar Dakarun Sojojin Nijeriya sashen jami’an Ordnance Corps (NAOC), ta sanar da neman ɗaya daga cikin jami’anta ruwa a jallo kan zargin sa da hannu a sayarwa da samar da kakin sojoji ga ‘yan ta’adda da wasu masu aikata miyagun laifuka.

Bincike ya nuna cewa, sojan, wanda yake aiki a sashen masana’antar haɗa kayan sojoji, ya bar wajen aikinsa ne tun a ranar 3 ga watan Yuni, 2026 domin guje wa kamu.

A wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na sojoji, Manjo Oluwatope Aluko ya fitar a ranar Alhamis, ya ce an ayyana jami’i Mohammed Yusuf Amutu ne a matsayin wanda ake nema bisa zargin sa da sayar da kayan inifom ɗin sojoji ga ‘yan ta’adda da kuma aika musu.

A cewarsa, ana bincike domin ganin an kamo shi don ya fuskanci hukuncin dokokin sojoji da na farar hula yayin da aka tabbatar da laifin akansa.

Akan haka ne rundunar ta roƙi al’umma da su taimaka wa binciken sojoji wajen bayar da bayanan da za su taimaka wa ƙoƙarin cafko sojan ta hanyar sanar da ofishi mafi kusa.

By Babaji

Leave a Reply