
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Gwamnan Jihar Nasarawa, Abdullahi Sule, ya yi wani ƙaramin garambawul ga tawagar manyan jami’an gwamnatinsa.
Sakataren Gwamnatin jihar, Dakta Shuaibu Labaran Magaji ne ya bayyana haka jim-kaɗan bayan kammala zaman majalisar zartarwar gwamnatin a ranar Talata, 22 ga Yuli, 2026 a Lafia.
A cewarsa, gwamnan ya ce sauye-sauyen wani ɓangare ne na ƙoƙarin ƙarfafa shirye-shiryen gwamnatin na tunkarar babban zaɓen 2027 da ke cigaba da ƙaratowa.
Ya sanar da cewa, kwamishinoni guda shida ne aka sauke daga muƙaminsu, waɗanda suka haɗa da kwamishinan lamuran tsaro, Usman Baba, kwamishinan filaye, David Moyi, kwamishinar harkokin mata da ci-gaban al’umma, Hauwa Jigbo da kwamishinan kimiyya da fasaha, Gabriel Agbashi.
Haka kuma, akwai kwamishinan yaɗa labarai, al’adu da walwala Ibrahim Tanko.
Gwamnatin ta kuma yaba wa jami’an da matakin ya shafa bisa ƙoƙarinsu na tabbatar da shugabanci na gari, tana mai cewa za ta bayyana sunayen waɗanda za su maye gurbinsu a lokacin da ya dace.
