Umarnin harbe ’yan ta’adda da zarar an gan su da kuma batun afuwa gare su

Spread the love

Umarnin da Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa (mai ritaya), ya bai wa dakarun sojin Nijeriya na su harbe ’yan ta’adda, ’yan bindiga, masu garkuwa da mutane da sauran masu aikata manyan laifuka da zarar sun hango su ba tare da jiran wani umarni ba, mataki ne da ya dace. A zahiri, wannan mataki ya kamata ya zo tun shekaru da suka gabata.

A wajen ƙaddamar da sabbin kayan tsaro da gwamnatin Jihar Sakkwato ta saya a makon da ya gabata, Ministan ya gargaɗi dakarun cewa duk wanda ya ƙi harbin ɗan ta’adda ko ɗan bindiga da hujjar yana jiran umarni daga sama, za a ɗauke shi tamkar mai haɗa baki da masu laifin.

Wannan matsaya ta zo ne a lokacin da Nijeriya ke ƙara ƙaimi wajen daƙile matsalar rashin tsaro, musamman a yankin Arewa maso Yamma, inda ’yan bindiga ke ci gaba da kashe mutane, yin garkuwa da su domin neman kuɗin fansa, satar shanu da kai hare-hare kan al’ummomin manoma.

A wannan taro ne gwamnatin Jihar Sakkwato ta ƙaddamar da kayan tsaro da suka kai darajar sama da Naira biliyan 27 domin tallafa wa jami’an tsaro. Kayan sun haɗa da motoci masu sulke, motocin sintiri, babura, rigunan kariya daga harsasai da sauran kayan aiki da ake sa ran za su ƙara wa jami’an tsaro ƙarfi wajen gudanar da ayyukansu.

Gwamnan Jihar Sakkwato, Ahmed Aliyu, ya bayyana cewa saka hannun jarin da gwamnatinsa ta yi a fannin tsaro na nuna irin muhimmancin da take bai wa dawo da zaman lafiya, yana mai cewa babu ci gaban tattalin arziki ko noma mai ɗorewa idan babu tsaro.

Shi kuwa Ministan Tsaro ya yaba da wannan ƙoƙari, tare da jaddada muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro, gwamnatoci da al’ummomi wajen tattara bayanan sirri da yaƙi da masu aikata laifuka.

Lokacin sassauci ya ƙare:

A ra’ayinmu, wannan umarni alama ce ta sauyin salo a yaƙin da ake yi da ’yan ta’adda da sauran masu aikata manyan laifuka. Ya nuna cewa gwamnati ta fahimci cewa ba za a iya ci gaba da nuna sassauci ga waɗanda suka shafe sama da shekaru goma sha biyar suna gallaza wa ’yan Nijeriya ba.

A irin wannan yaƙi, babu wata mafita ta tsaka-tsaki. Ko dai jami’an tsaro su kawar da barazanar, ko kuma su bar masu laifin su ci gaba da cin karensu babu babbaka.

Hakazalika, muna goyon bayan matsayar Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai na dakatar da shirin Kwance ɗamara, Rushe Tsarin Mayaƙa, Gyaran Hali, Sake Shigar da Su Cikin Al’umma da Sulhu (DDRRR) da ake aiwatarwa ga waɗanda ake kira tubabbun ’yan Boko Haram, ISWAP, ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane.

Wannan matsaya ta biyo bayan ƙudurin da shugaban Kwamitin Sojoji na Majalisar Dattawa, Sanata Abdulaziz Yar’Adua, ya gabatar, sakamakon ci gaba da hare-haren da ake kai wa jami’an tsaro masu aiki da waɗanda suka yi ritaya, da kuma sauran ’yan ƙasa.

A ra’ayinmu, babu dalilin da zai sa mutum ya kashe mutane, ya lalata garuruwa, ya raba dubban iyalai da muhallansu, daga baya kuma a ce an yafe masa tare da mayar da shi cikin al’ummar da ya yi wa ta’asa.

Ina adalci ga waɗanda aka zalunta?

Babbar tambayar da ya kamata gwamnati ta amsa ita ce: idan ana yafewa masu aikata irin waɗannan munanan laifuka, ina adalci ga dubban mutanen da suka rasa rayukansu? Me gwamnati ta tanadar wa iyalan waɗanda aka kashe ko aka jikkata?

Rahotanni sun nuna cewa sama da mutum dubu 35 ne suka rasa rayukansu, yayin da fiye da mutum miliyan biyu suka rasa matsugunansu tun bayan fara rikicin Boko Haram shekaru 16 da suka gabata.

Masu goyon bayan wannan shirin na yawan kwatanta shi da shirin afuwar da gwamnatin marigayi Shugaba Umaru Musa Yar’Adua ta bai wa mayaƙan Neja Delta a shekarar 2009.

Sai dai akwai babban bambanci tsakanin mayaƙan Neja Delta, wadanda suka yi iƙirarin neman adalci ga yankinsu, da kuma ’yan ta’adda da ’yan bindiga, waɗanda manufarsu ita ce kashe jama’a, sace mutane domin kuɗin fansa, lalata al’umma da yaɗa tsattsauran ra’ayi.

Abin da ya fi tayar da hankali shi ne yadda ake ba wasu daga cikin waɗanda ake kira tubabbun ’yan ta’adda damar shiga cikin rundunonin tsaro da sunan cewa za su taimaka wajen gano maɓoyar sauran masu laifi.

A ra’ayinmu, wannan tsari na da haɗari ƙwarai. Kamar yadda ƙarin magana ke cewa, ba a shuka iri ana rakiyar zakara ba. Duk wanda ya aikata laifi ya kamata ya fuskanci hukuncin doka kafin a yi tunanin wata afuwa ko sassauci.

Saboda haka, muna mara wa Majalisar Dattawa da Majalisar Wakilai baya cewa duk wani ɗan ta’adda, ɗan bindiga ko mai garkuwa da mutane dole ne a gurfanar da shi a gaban kotu, kuma idan aka same shi da laifi ya fuskanci cikakken hukuncin doka.

Manufar “je ka, Allah Ya yafe maka” ba wai kawai tana tauye haƙƙin waɗanda aka zalunta ba ne, har ma tana ƙarfafa sauran masu aikata laifuka su ci gaba da ta’asa cikin tunanin cewa daga ƙarshe za a yafe musu.

A ƙarshe, tuba abu ne mai kyau a addini, amma a tsarin mulki da doka, tuba ba ta soke hukuncin laifin da aka aikata. Adalci ga waɗanda aka zalunta dole ne ya kasance ginshiƙin duk wata manufar gwamnati wajen yaƙi da ta’addanci da sauran manyan laifuka.

By ukarofi

Leave a Reply