
Shugaba Bola Tinubu ya amince da faɗaɗa tsarin Rundunar Sojin Nijeriya daga rundunoni takwas zuwa 12 tare da ɗaukar sabbin sojoji 28,000 domin ƙarfafa tsaron ƙasa.
Sanarwar da Kakakinsa Bayo Onanuga, ya fitar a ranar Alhamis ta ce matakin zai inganta jagoranci da gudanar da ayyukan soja, ƙarfafa tsaron kan iyakoki, kare muhimman ababen more rayuwa, da kuma haɓaka yaƙi da ta’addanci da sauran matsalolin tsaro.
Sabbin rundunonin za su kasance a Makurɗi, Ilorin, Jalingo da Benin City, yayin da za a aiwatar da sabon tsarin kashi biyu.
Kashi na farko zai kammala nan da watan Satumban 2026, yayin da na biyu zai kammala zuwa watan Disamban 2026.
Shugaba Tinubu ya kuma yabawa Babban Hafsan Sojin Ƙasa, Laftanar Janar Waidi Ibrahim Shuaibu, da dakarun rundunar bisa jajircewarsu wajen kare haɗin kan Nijeriya da tsaron ƙasar.
