KASOSA ta kai shekara 40 cikin haɗin kai da tallafa wa mambobinta – Farfesa Ali Abdullahi

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano

Tsohon Shugaban ƙungiyar Tsofaffin ɗaliban Makarantar Kimiyya da Fasaha ta Kano (KASOSA), Farfesa Ali Abdullahi, ya yabawa aji na shekarar 1986 bisa yadda suka ci gaba da haɗa kan mambobi da gudanar da ayyukan taimakon juna.

Ya bayyana hakan ne yayin bikin cika shekaru 40 da kammala makarantar da aka gudanar a Jami’ar Northwest da ke Kano.

Farfesa Ali ya ce aji na 1986 ya zama abin koyi wajen sada zumunci, tallafa wa tsofaffin ɗalibai masu buƙata da kuma kula da iyalan waɗanda suka rasu.

Ya yi kira ga sauran ƙungiyoyin tsofaffin ɗalibai su yi koyi da irin wannan haɗin kai domin ci gaban al’umma.

Shi ma Dakta Ali Abdu Gezawa ya ce ci gaba da ziyartar malamai da makaranta tare da gudanar da ayyukan alheri ya nuna muhimmancin haɗin kai tsakanin tsofaffin ɗalibai.

By ukarofi

Leave a Reply