Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano
ƙungiyar Kano Association Council of Traders and Entrepreneurs (KASCOTE) ta gudanar da taronta na uku a Kano, inda ta haɗa ‘yan kasuwa da masu zuba jari daga sassa daban-daban na Nijeriya da ƙasashen waje domin bunƙasa harkokin kasuwanci da masana’antu.
Shugaban KASCOTE, Alhaji Hassan Yaro, ya bayyana a wajen buɗe taron cewa manufar taron ita ce ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin ‘yan kasuwa, da samar da damar zuba jari da bunƙasa masana’antu.
Ya ce taron baje kolin kayayyaki ya samu haɗin gwiwa da Jamhuriyar Indonesia, ƙarƙashin jagorancin jakadan ƙasar a Nijeriya, tare da rakiyar shugabannin jami’o’i biyu daga Indonesia domin tattauna hanyoyin ba ɗaliban Nijeriya damar samun guraben karatu da kuma ƙarfafa alaƙar kasuwanci.
Daga cikin waɗanda suka halarci taron akwai shugabannin kamfanonin NIBG, ciki har da Hon. Uchenna Heris Okonkwo da Daraktan Kamfanin Godspower Isiguzo, waɗanda suka bayyana cewa taron zai ƙara bunƙasa tattalin arzikin Kano da Nijeriya baki ɗaya.
Sauran mahalarta taron sun haɗa da shugaban Salaha Commodity, Alhaji Mudassir Mansur Bala; Abdussalam Mustapha (Indomie Kano); da Masa’ud Amajara.
A nasa jawabin, wakilin Sarkin Kano, Farfesa Abubakar Aminu Sunusi Bayero, ya ce irin wannan haɗin gwiwa tsakanin KASCOTE da ƙasashen waje zai taimaka wajen bunƙasa tattalin arzikin Kano da Nijeriya, tare da ƙarfafa alaƙar kasuwanci da ilimi.
