Ba zan soki Tinubu a talabijin ba alhali Ina da damar ba shi shawara a sirrance – Fashola

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Tsohon Gwamnan Jihar Legas, kuma tsohon Ministan Ayyuka da Gidaje na Tarayya, Babatunde Raji Fashola, ya bayyana cewa ba ya da niyyar sukar gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu a bainar jama’a, yana mai cewa ya fi son ci gaba da ba shugaban ƙasar shawarwari kai tsaye a sirrance.

Fashola ya bayyana haka ne yayin wata hira da ya yi da tashar yaɗa labarai ta TVC a ranar Laraba, inda ya amsa tambayoyi kan dalilin da ya sa ba kasafai yake yin tsokaci a fili game da yadda gwamnatin Tinubu ke tafiyar da mulki ba.

A cewarsa, Shugaba Tinubu na yawan neman shawararsa kan harkokin mulki da kuma abubuwan da gwamnati za ta inganta yayin da ake tunkarar babban zaɓen shekarar 2027.

Ya ce, idan shugaban ƙasa ya kira shi ya tambaye shi abin da ya kamata gwamnatinsa ta gyara, bai dace ya fito yana ba da irin wannan shawara a talbijin ba.

“Idan shugaban ƙasa ya kira ni ya ce na faɗi wani fanni da gwamnatinsa ya kamata ta inganta yayin da ake shirin 2027, shin zan fito ina ba shi amsa ta talbijin ne? Na yanke shawarar ba zan yi haka ba,” inji Fashola.

Tsohon ministan ya bayyana cewa ya riga ya ba Shugaba Tinubu shawarwari kan batutuwa da dama, yana mai cewa ci gaba da kasancewa da wannan damar tattaunawa kai tsaye ya fi muhimmanci a gare shi fiye da yin kalamai a kafafen yaɗa labarai.

Ya ce, yana iya ganawa da shugaban aasa duk lokacin da buƙatar hakan ta taso, saboda haka ba ya ganin akwai wata fa’ida wajen mayar da shawarwarinsa abin tattaunawa a talbijin.

Da aka tambaye shi ko gwamnatin Tinubu ta fara rasa hangen nesa bayan kusan shekara uku a mulki, Fashola ya yi watsi da wannan ra’ayi.

Ya ce, kasancewarsa cikin mutanen da shugaban ƙasa ke sauraron su ya sa ba shi da dalilin yin suka a bainar jama’a.

“Ba za ka riƙa yi wa mutumin da yake saurararka ihu ba,” inji shi.

Fashola ya kuma yi watsi da raɗe-raɗin cewa yana da burin tsayawa takarar shugaban ƙasa nan gaba. Da aka tambaye shi kai tsaye ko yana da wannan buri, ya amsa da cewa: “A’a.”

Lokacin da aka sake matsa masa da tambayar shugaban ƙasar wace ƙasa yake nufi, sai ya yi murmushi ya ce: “Shugaban wace ƙasa? Ni shugaban gida na ne.” Ya ce, hidimar gwamnati abin alfahari ne.

Fashola ya bayyana cewa damar da ya samu ta yi wa Nijeriya hidima sama da shekara 20 abin alfahari ne a gare shi, yana mai fatan hakan zai ƙarfafa matasa su shiga harkar aikin gwamnati domin bayar da tasu gudunmawa wajen gina ƙasa.

Tsohon gwamnan ya ƙi yin tsokaci kan jita-jitar da aka daɗe ana yi cewa ya fi son Obafemi Hamzat ko Olasupo Sasore su gaje shi a zaɓen gwamnan Legas na shekarar 2015.

Sai dai ya tabbatar da cewa har yanzu shi mamba ne a Majalisar Ba da Shawara kan Mulkin Jihar Legas (GAC). Ya ce aikin majalisar shi ne bayar da shawara kawai, ba tsoma baki cikin tafiyar da gwamnati ba. A cewarsa, akwai bambanci tsakanin bayar da shawara da kuma katsalandan cikin harkokin gwamnati.

By ukarofi

Leave a Reply