Jami’o’in Indonesiya biyu sun nemi haɗin gwiwa da Jami’ar KHAIRUN

Spread the love

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano

Shugabannin jami’o’in MANGKURAT da AIRLANGGA na ƙasar Indonesia sun ziyarci Khalifa Isyaku Rabiu University (KHAIRUN) da ke Kano domin tattauna yiwuwar ƙulla yarjejeniyar haɗin gwiwa a fannin ilimi.

Shugaban Jami’ar MANGKURAT, Farfesa Ahmad Alim Bachri, ya ce binciken da suka gudanar kan ayyukan KHARUN ne ya sa suka ga dacewar fara haɗin gwiwa da jami’ar.

A nasa jawabin, Mataimakin Shugaban KHAIRUN, Farfesa Abdurrashid Garba, ya ce jami’ar a shirye take ta yi aiki tare da duk wata cibiyar ilimi da ke da muradin bunƙasa bincike da koyarwa.

Ya ƙara da cewa KHARUN ta ginu ne kan ginshiƙai huɗu da suka haɗa da ilimi, tarbiyya, koyar da Alƙur’ani Mai Girma da kuma bunƙasa harkokin kasuwanci na zamani.

Taron ya samu halartar wakilan Jakadancin Indonesia a Nijeriya da kuma shugabannin KASCOTE.

By ukarofi

Leave a Reply