Wani magidanci ya roƙi kotu ta tilasta wa ’yarsa fitar da mijin aure

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Wani magidanci mai ’ya’ya 11, Lawal Hamisu, ya garzaya Kotun Shari’a ta II da ke zamanta a Magajin Gari, Jihar Kaduna, inda ya roƙi kotun da ta umarci ’yarsa mai suna Fatima Lawal ta gabatar da wanda zai aure ta, tare da taimaka wajen ɗaura musu aure.

Ta bakin lauyansa, H.B. Debo, Lawal ya shaida wa kotun cewa Fatima mai shekara 27, wadda ta kammala karatun Babbar Difloma (HND), har yanzu ba ta gabatar da wani namiji da ya zo neman aurenta ba.

Ya ce duk da cewa ’yarsa tana da samari, babu wanda ya taɓa zuwa gidan su domin neman aurenta a hukumance.

“Ina roƙon kotu ta ba ta umarnin ta samo wanda zai nemi aurenta, ta gabatar da shi a gaban kotu, sannan kotun ta taimaka wajen ɗaura musu aure. Tun da mahaifiyarsu ta gurɓata tunanin ’ya’yanmu a kaina,” inji Lawal.

Da take mayar da martani, Fatima ta shaida wa kotun cewa har yanzu babu wani saurayi da ya zo neman aurenta da gaske.

Ta ce duk da cewa tana da samari, babu wanda ya gabatar da buƙatar aure a hukumance.

Alƙalin kotun, Malam Yakubu Abdullahi, ya bayyana cewa shari’ar na da muhimmanci domin ta shafi alaƙar uba da ’yarsa.

Ya ce zai tattauna da kowanne ɓangare daban domin gano musabbabin rikicin kafin ya yanke hukunci ko ba da shawarar da ta dace.

Kotun ta ɗage sauraron shari’ar zuwa ranar 3 ga Agusta, domin ci gaba da sauraro da yanke hukunci.

By ukarofi

Leave a Reply