Amurka ta kashe Dala miliyan 1.2 wajen kare kayan tarihin Nijeriya

Spread the love

Daga MAHDI MUSA NUHAMMAD

Gwamnatin Amurka ta bayyana cewa ta kashe Dala miliyan 1.2 cikin shekaru biyar da suka gabata wajen tallafa wa ayyukan kare kayan tarihi da al’adun gargajiya a jihohi 21 na Nijeriya, tana mai cewa wannan ba tallafi kawai ba ne, illa wata dabarar zuba jari da ke amfanar ƙasashen biyu.

Mataimakin Jakadan Amurka a Nijeriya, Keith Heffern, ne ya bayyana hakan ranar Talata yayin ƙaddamar da wani aikin kare kayan tarihi da Gidauniyar Wheyham ta gudanar a Abuja.

A cewarsa, kuɗaɗen da aka kashe sun fito ne musamman daga Asusun Jakadun Amurka na Kare Kayan Tarihi, wanda ya taimaka wajen kare muhimman kayan tarihin Nijeriya tare da ƙarfafa dangantakar ƙasashen biyu.

Heffern ya ce, cikin shekaru biyar, an yi nasarar adana fiye da kayayyakin tarihi 250 na wayewar Nok ta hanyar fasahar zamani, an gyara gidan adana kayan tarihin Nok, an horar da matasa 50 ‘yan Nijeriya kan sabbin dabarun fasahar zamani, yayin da sama da mutum 50,000 suka amfana da shirye-shiryen wayar da kai a faɗin ƙasar.

Ya ƙara da cewa, an gina tsarin ne da fasahar Amurka, wanda ya samar da sakamako mai ɗorewa wajen kare kayan tarihi da kuma bunƙasa haɗin gwiwa tsakanin ƙasashen biyu.

Mataimakin Jakadan ya bayyana cewa tsarin ya kuma ƙunshi fasahar NFT (Non-Fungible Token) domin bibiyar kayan tarihi ta hanyar dijital, da nufin hana safarar su ba bisa ƙa’ida ba da kuma ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin hukumomin tsaro na Nijeriya da Amurka.

A cewarsa, wannan fasaha za ta taimaka wajen daƙile ƙungiyoyin masu safarar kayan tarihi ba bisa ƙa’ida ba, waɗanda ke gudanar da harkokin da darajarsu ta kai biliyoyin daloli.

Ya ce, kare kayan tarihin Nijeriya na da amfani ga Amurka, domin hakan na taimakawa wajen karya hanyoyin ayyukan ƙungiyoyin masu laifi tare da samar da ingantacciyar makoma ga ƙasashen biyu.

Da take jawabi a wajen taron, Ministar Fasaha, Al’adu, Yawon Buɗe Ido ta Nijeriya, Hannatu Musawa, ta bayyana ƙaddamar da tsarin dijital na tarihin Nok a matsayin cika wani muhimmin ɓangare na yarjejeniyar kiyaye kayan tarihi da Nujeriya da Amurka suka rattaba hannu a kanta a shekarar 2025.

Ta tuno cewa a watan Fabrairun shekarar da ta gabata ta sanya hannu kan yarjejeniyar tallafi tsakanin ma’aikatarta da Ofishin Jakadancin Amurka, ƙarƙashin Asusun Jakadun Amurka na Kare Kayan Tarihi, domin tattarawa da kare gumakan Nok na ƙasa da aka tono a Jihar Kaduna.

Musawa ta bayyana wayewar Nok a matsayin ɗaya daga cikin tsofaffin cibiyoyin fasaha mafiya daraja a Afirka, tana mai cewa gumakan laka da mutanen Nok suka ƙera sun wanzu tun ƙarnuka kafin haihuwar Annabi Isa (A.S.).

Ta ce, shekaru da dama tarihin Nok ya taƙaitu ne a gidajen adana kayan tarihi da kuma binciken masana, amma haɗin gwiwar Gidauniyar Wheyham da Hukumar Kula da Gidajen Tarihi da Kayan Gargajiya ta ƙasa (NCMM) da Jami’ar Yale ya kawo sauyi wajen bayyana wannan tarihi ga duniya.

Ministar ta jaddada cewa amfani da fasahar dijital ba zai maye gurbin aikin kare kayan tarihi a zahiri ba, sai dai zai tabbatar da cewa tarihin Nijeriya ya isa ga mutanen da ba za su samu damar kai ziyara Kaduna ba, tare da kiyaye bayanansa ko da wani abu ya faru da kayan tarihin.

Ta kuma bayyana cewa gwamnati na shirin faɗaɗa irin wannan aiki zuwa sauran wuraren tarihi da al’adun gargajiya a faɗin ƙasar, tana mai yabawa Amurka bisa fiye da shekaru ashirin da take bayar da gudunmawa wajen kare kayan tarihin Nijeriya.

Shi ma da yake jawabi, Ministan Tsaro, Janar Christopher Musa (mai ritaya), ya ce kare tarihin al’umma na taka muhimmiyar rawa wajen ƙarfafa tsaro, haɗin kai da kuma martabar ƙasa.

Ya bayyana cewa tsaron ƙasa ba ya taƙaitu ga ƙarfin sojoji kaɗai, domin al’ummar da suka san tarihinsu, asalinsu da kuma abin da suka tsaya a kai su ne ke gina ƙasa mai ɗorewa.

Janar Musa, wanda ɗan asalin ƙaramar Hukumar Zangon Kataf ta Jihar Kaduna ne, ya bayyana wayewar Nok a matsayin gadon tarihi na dukkan ‘yan Nijeriya, tare da yin kira da a ƙara ƙaimi wajen kare kayan tarihi daga sata, safarar haramtacciya, lalata da kuma sakaci.

A lokaci guda, ministocin biyu sun yaba wa Gidauniyar Wheyham, Ofishin Jakadancin Amurka, Jami’ar Yale da Hukumar NCMM saboda amfani da shirye-shiryen fina-finai da fasahar zamani wajen kusantar da tarihin Nok ga matasan Nijeriya da sauran al’ummar duniya.

A nasa jawabin, Shugaban Gidauniyar Wheyham, Malam Yahaya Maikori, ya ce aikin ya haɗa dabarun gargajiya da fasahar zamani domin inganta kare kayan tarihi, sauƙaƙa samun bayanansu da kuma bunƙasa yawon buɗe ido na al’adu.

By ukarofi

Leave a Reply