An rantsar da sabbin shugabannin ANCOPSS a Kano

Spread the love

Daga IBRAHIM MUHAMMAD a Kano

An rantsar da sabbin shugabannin ƙungiyar Shugabannin Makarantun Sakandare ta Jihar Kano (ANCOPSS), tare da raba magungunan agajin gaggawa ga makarantun kwana 20 da ke faɗin jihar.

Da yake jawabi a wajen taron, Sakataren Gudanarwa na Hukumar Kula da Makarantun Sakandare ta Jihar Kano, Alhaji Rabiu Saleh Gwarzo, ya buƙaci sabbin shugabannin da aka rantsar su mayar da hankali wajen inganta shugabancin makarantu tare da tabbatar da haɗin kai a tsakanin membobin ƙungiyar.

Ya ce haɗin kai shi ne ginshiƙin nasara, yana mai bayyana cewa idan shugabannin makarantu suka kasance “tsintsiya maɗaurinki ɗaya”, hakan zai taimaka wajen bunƙasa harkar ilimi da kuma inganta gudanar da makarantun sakandare a jihar.

Alhaji Rabiu Saleh Gwarzo ya taya sabbin shugabannin murnar kama aiki, tare da yi musu alƙawarin ba su cikakken haɗin kai domin tabbatar da an cimma manufofin da aka sanya a gaba.

Da yake magana kan rabon magungunan, ya bayyana cewa shirin ya samo asali ne daga ƙoƙarin Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, na inganta harkar ilimi da walwalar ɗalibai.

A cewarsa, yawancin makarantun kwana suna da nisa da cibiyoyin lafiya, lamarin da ke janyo tsaiko wajen kai ɗalibai asibiti idan suka kamu da rashin lafiya.

“Mun samar da waɗannan magunguna ne domin a riƙa ba da agajin gaggawa ga ɗalibai kafin a kai su asibiti domin samun cikakkiyar kulawa,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa makarantun kwana 20 ne za su amfana da wannan tallafi, tare da yin kira ga shugabannin makarantu da su kula da magungunan yadda ya kamata, kuma su tabbatar ana amfani da su wajen taimaka wa ɗaliban da suka shiga halin buƙatar kulawar gaggawa.

A nasa jawabin, sabon Shugaban ANCOPSS na Jihar Kano, kuma Shugaban Makarantar Sakandaren Gwamnati ta Dala, Kwamared Halliru Inuwa, ya bayyana farin cikinsa da amincewar da aka ba su na jagorantar ƙungiyar.

Ya ce sabuwar shugabancin za ta mayar da hankali wajen ƙarfafa haɗin kai tsakanin shugabannin makarantun sakandare domin tallafa wa manufofin gwamnatin jihar na bunƙasa ilimi.

Kwamared Halliru Inuwa ya jaddada cewa babu wata ƙungiya da za ta ci gaba ba tare da karɓar shawarwari masu amfani ba.

“ƙofata a buɗe take ga duk wata shawara mai amfani. Muna buƙatar haɗin kai domin mu ne ke da alhakin tarbiyya da jagorancin ɗalibai. Idan muka haɗa kai, za mu iya cimma duk wata manufa da muka sanya a gaba,” inji shi.

By ukarofi

Leave a Reply