Inganta ilimi shi ne babban abin da na sanya a gaba, inji Hon. Balago

Spread the love

Daga SULEIMAN HUSSAINI D/KUDU a Kano

Shugaban ƙaramar Hukumar Kiyawa da ke Jihar Jigawa, Hon. Abdulhamid Ibrahim Balago, ya ce inganta ilimi shi ne babban abin da gwamnatinsa ta bai wa fifiko, yana mai jaddada cewa ilimi shi ne ginshiƙin ci gaban al’umma a kowane fanni.

Balago ya bayyana hakan ne yayin da yake zantawa da manema labarai a wajen bikin yaye dalibai karo na takwas da kuma rabon kyaututtuka da aka gudanar a Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke Kiyawa a makon da ya gabata.

Ya ce tun bayan hawansa mulki ya kafa kwamitin bunkasa ilimi karkashin jagorancin mataimakinsa, tare da haɗin gwiwar masu ruwa da tsaki a bangaren ilimi, domin gano matsalolin da ke addabar makarantu da kuma samar da hanyoyin magance su.

A cewarsa, binciken da kwamitin ya gudanar a dukkan mazabu 12 na karamar hukumar ya gano ɗalibai 444 da ke da matsaloli musamman a darussan Turanci da Lissafi.

Ya bayyana cewa gwamnati ta dauki nauyin karatun ɗalibai 222 daga cikinsu, sannan daga baya majalisar karamar hukumar ta sake biya wa wasu ɗalibai 12 kudin sake rubuta jarabawar NECO, inda kusan kashi 90 cikin 100 suka samu nasara.

Shugaban ƙaramar Hukumar ya kara da cewa gwamnatin ta dauki nauyin karatun ɗalibai 62 ‘yan asalin Kiyawa a Kwalejin Ilimi ta Tarayya da ke Azare a Jihar Bauchi har zuwa kammala karatunsu.

Haka kuma, ya ce an dauki nauyin karatun ɗalibai 30 a Makarantar Koyon Aikin Lafiya da ke Gwaram, inda ya bayyana cewa gwamnatin karamar hukumar ta kashe kimanin naira miliyan 30 wajen biyan kudin karatun nasu.

Balago ya ce a bana ma gwamnatin ta biya kudin jarabawar JAMB ga ɗalibai 100, yayin da ta biya wa ɗalibai 150 kudin jarabawar NECO.

Ya kuma bayyana cewa majalisar karamar hukumar na daukar nauyin karatun ɗalibai 50 ‘yan asalin yankin da ke karatu a Kwalejin Koyon Aikin Shari’a da ke Ringim.

Ya ce gwamnatin za ta ci gaba da tallafa wa ɗaliban da ke bukatar sake rubuta jarabawar NECO domin inganta sakamakonsu.

Kazalika, ya bayyana cewa an samar da litattafai sama da 25,000 da aka raba wa makarantun firamare da sakandare da ke fadin karamar hukumar domin bunkasa harkar ilimi.

Bugu da kari, ya ce gwamnatin ta kashe sama da naira miliyan 1.55 wajen buga takardun shaidar kammala karatu ga ɗaliban da suka kammala karatunsu.

Hon. Abdulhamid Ibrahim Balago ya tabbatar da cewa gwamnatin Karamar Hukumar Kiyawa za ta ci gaba da bai wa bangaren ilimi fifiko, yana mai cewa ci gaban ilimi shi ne mabuɗin ci gaban al’umma da ƙasa baki ɗaya.

By ukarofi

Leave a Reply