Daga ABUBAKAR A BOLARI Gombe
Babbar Kotun Tarayya mai lamba ta ɗaya da ke zamanta a Gombe ta umarci hukumar tsara da kula da bayanai kan filaye ta Jihar Gombe (GOGIS) da tsohon darakta janar nata, Kabiru Usman Hassan, su miƙa takardun da suka shafi aikin sake fasalin Shehu Abubakar Layout ga wani ɗan ƙasa da ya nemi bayanan bisa dokar ’yancin samun bayanai (FOI) ta shekarar 2011.
Mai Shari’a Amina Aliyu Mohammed ta yanke hukuncin ne bayan ta tabbatar da cewa GOGIS ba ta amsa buƙatar Nafi’u Abubakar cikin wa’adin kwanaki bakwai da dokar ta tanada ba, lamarin da kotun ta ce ya sa aka ɗauki hukumar a matsayin ta ƙi bayar da bayanan.
Kotun ta umarci GOGIS da tsohon darakta janar nata su miƙa dukkan takardun da suka shafi aikin cikin kwanaki 14.
Ta kuma ce idan akwai wasu takardun da ba za a iya bayarwa ba, dole ne su bayyana hakan a rubuce tare da dalilan da dokar FOI ta tanada.
Sai dai kotun ta yi watsi da buƙatar a biya mai ƙarar diyyar naira miliyan 100, tana mai cewa manufar dokar FOI ita ce tabbatar da gaskiya da bai wa jama’a damar samun bayanai, ba wai hukunta hukumomin gwamnati da tara ba.
Duk da haka, kotun ta umarci GOGIS da tsohon darakta janar nata su biya Nafi’u Abubakar kuɗin shari’a har naira 200,000.
