Ra’ayi

Ina za a samu hoton Narambaɗa?

Ina za a samu hoton Narambaɗa?

Daga IBRAHIM SHEME Malam Ibrahim Buhari Maidangwale Abdulƙadiri Tubali, wanda aka fi sani da Ibrahim Narambaɗa, fitaccen makaɗin Hausa ne wanda ya rayu a tsakanin wajajen 1890 da Disamba, 1963. Ya yi waƙoƙi masu tarin yawa inda ya wasa sarakuna a ƙasashen Hausa da dama, irin su Zamfara da Maraɗi da Zazzau. Duk da yake a fagen waƙar sarauta ya fi yin fice, ya yi waƙoƙin noma da na ma'aikata (alƙalai) da na 'yan siyasa irin su Sardauna Ahmadu Bello da na sha'awa (misali waƙar 'Dokin Iska Ɗanhilinge'). An yi ittifaƙi da cewa ya na da zurfin basira, ta yadda…
Read More
Raud al-jinan: Gudunmawar Waziri Gidado bin Laima

Raud al-jinan: Gudunmawar Waziri Gidado bin Laima

Tare da FATUHU MUSTAPHA Kwanakin baya, Farfesa Malumfashi Ibrahim ya janyo hankalina a wani rubutu da wani masani daga Kasar Amurka: Hui Xinpeng ya yi a kan shahararren littafin nan da Wazirin Sokoto : Gidado bin Laima ya rubuta a kan karamomim Shehu Usman bin Fodio, wannan rubutu ya burgeni, kuma har na kwafa na sanya shi a bango na na Facebook. To Amma ba wannan ne ya dauki hankali na ba, wani abu ne ya faru wasu mutum biyu daga cikin mutanen da suka yi koment a kan bayanin, sun kira littafin da tatsuniya: wannan abu ya bani mamaki…
Read More
Misalin da Sheikh Ahmad Gumi ya kafa

Misalin da Sheikh Ahmad Gumi ya kafa

Tare da IBRAHIM SHEME Ba kasafai Sheikh Dakta Ahmad Gumi ya kan nasa kwan sa ba tare da zakara ba; manufa, ba ya magana ko aikata wani abu ba tare da kwakkwarar hujja ba. Sau da yawa, kalaman sa ba su yi wasu dadi saboda an saba da son jin magana mai dadi, musamman wajen voye gaskiya tare da zama a kan akasin ta. Dakta Gumi ya sha yin suka kan halin rashin tsaro da ake ciki a kasar nan, musamman a Arewa. Kuma ya sha yin nuni da hanyar da ya kamata a bi domin a bulle zuwa inda…
Read More
Shin ya dace a taya daliban Kankara murnar sace su?

Shin ya dace a taya daliban Kankara murnar sace su?

Tare da NASIRU ADAMU EL-HIKAYAWannan tambaya ce da ni marubuci na yi wa kai kuma na ke son ba da amsa da kai na. Da farko ma na so kai tsaye na radawa rubutun nan suna "Ina taya daliban Kankara murnar sace su!." Gaskiya zai iya yin ma'ana idan a ka ce sace 'yan makarantar nan da duk alamu ke nuna 'ya'yan talakawa ne ya jawo hankalin duniya ya koma kan su. Hatta mutan kudancin Najeriya sun ciccije sun koyi yanda a ke furta Kankara a jihar Katsina. Yanzu ka na shiga yanar gizo ka rubuta Kan...a injin bincike za…
Read More
Ciyaman Nda-Isaiah: Ba rabo da gwani ba…

Ciyaman Nda-Isaiah: Ba rabo da gwani ba…

Daga IBRAHIM SHEME Tun a ranar farko da na fara haduwa da Mista Sam Nda-Isaiah, cikin mintuna kadan, ya dauke ni aiki. A lokacin ya na fafutikar neman wani qwararre wanda zai nada editan sabuwar jaridar sa mai suna LEADERSHIP, har wani tsohon dan jarida ya ba shi suna na. Rannan ya je Sakkwato domin nuna wa Gwamna Attahiru Bafarawa jaridar tasa, sai su ka hadu da wani aboki na a ofishin da su ke jira a yi wa kowannen su iso, domin ba tafiyar su daya ba, ba su ma san juna ba. Su na labari, sai abokin nawa…
Read More
Abota ita ce auren zamani

Abota ita ce auren zamani

Tare da AISHATU GIDADO IDRIS Zai iya yiwuwa ku kan yi wani tunani irin nawa, na cewar yawancin lokaci idan mutane ba su samu dama ko sa'ar auren wadanda su ke so ba, su kan samu aqalla wadanda su su ka fi alheri a gare su. Haka abin yake! Domin sau da yawa wasu su kan yi qorafin cewa rayuwa ta juya masu baya idan su ka rasa abin da su ka fi da so. Ba haka ba ne kuma. Tabbas, ana yawan auren soyayya, amma kuma ana yawan aure na sa'a, dace ko auren sakamako a kan rasa wani…
Read More
Qanqara- Tun da Garba ya nemi afuwa

Qanqara- Tun da Garba ya nemi afuwa

Tare da Nasiru Adamu El-Hikaya Muhawar yawan xaliban makarantar sakandaren Kankara a jihar Katsina da a ka sace ta zo qarshe tun da an gano yaran ko na ce an samu dukkan yaran har an ma miqa su ga iyayen su. Ba wata baquwar al’ada ba ce a Nijeriya a ba da labari da ya wuce kima ko ya gaza kima musamman hakan ya fi dogara ne ga yadda labarin ya shafi mai ba da shi. Hakanan a lokacin da gwamnati ko jami’an tsaro kan yi qoqarin rage kaifin labari don ta yiwu ya jawo tashin hankali ko zubar da…
Read More
Rikicin Addini: Salafiyya, Tijjaniya da Kadiriyya

Rikicin Addini: Salafiyya, Tijjaniya da Kadiriyya

Daga FATUHU MUSTAPHA A cikin makon da ya gabata ne, wasu manyan malaman salafiyya, wadanda suka hada da: Sheikh Muhammad bin Abdulwahab da Sheikh Dr. Mansur Sokkoto, suka yi kira ga gwamnatin jihar Kano da ta kama shehin malamin nan na darikar Qadiriya: Sheikh AbdulJabbar Nasiru Kabara. Wannan rigima dai ta samo asali ne, tun bayan da shi sheikh Abduljabbar ya fara wani tafsiri da ya kira Jauful Faraa. Tafsirin da mafiya akasarin malaman darikar ta Salafiya ke ganin ya saba qa’ida, ya na kuma wuce gona da iri. Wannan rigingimu dai ba yau aka fara fama da su, a…
Read More
Balarabe Musa: Gaba ta wuce…

Balarabe Musa: Gaba ta wuce…

Daga Ibrahim Sheme Alhaji Abdulqadir Balarabe Musa mutum ne “wani iri”. Ba a saba ganin irin sa ba. Mutum ne wanda idan an yi Yamma sai ya yi Gabas, idan kuma an yi Kudu shi sai ya yi Arewa. Wasu na kallon sa a matsayin murdadde, ba a yi tanqwasa shi a tattaunawar siyasa; wasu kuma na yi masa kallon mai sauqin kai, mai rungumar talakawa.Ko ma ta wace fuska mutum ya kalle shi, babu wanda zai ce maka ba nagartacce ba ne. Hatta mutanen da ya rayu ya na adawa da manufofin su sun yi ittifaqi da cewa ‘Bala…
Read More