Shin ya dace a taya daliban Kankara murnar sace su?

Tare da NASIRU ADAMU EL-HIKAYA
Wannan tambaya ce da ni marubuci na yi wa kai kuma na ke son ba da amsa da kai na. Da farko ma na so kai tsaye na radawa rubutun nan suna “Ina taya daliban Kankara murnar sace su!.” Gaskiya zai iya yin ma’ana idan a ka ce sace ‘yan makarantar nan da duk alamu ke nuna ‘ya’yan talakawa ne ya jawo hankalin duniya ya koma kan su. Hatta mutan kudancin Najeriya sun ciccije sun koyi yanda a ke furta Kankara a jihar Katsina. Yanzu ka na shiga yanar gizo ka rubuta Kan…a injin bincike za a karasa ma ka rubuta sunan cikekke don albarkacin wadannan yara da miyagun iri su ka sace su.Kazalika wata ribar ta sace yaran nan ita ce ta abun nan da Hausawa ke cewa dare daya Allah kan yi bature. A irin kasa kamar Najeriya da kawayen ta inda tsarin ‘yan jari hujja ya mamaye dukkan lamura, zai yi wuya ka ga wani ya taka wata rawar gaban hantsi matukar ba dan Sarki ba ne ko Dan Waziri. Hakanan ko ya zama dan wani tsohon Janar na soja ko babban sakatare zamanin turawa. Idan ka ga dan talakan talak ya yi fice to Allah ne ya kwata ya ba shi. Idan ku ba ku yi mamaki ba, to ni na yi mamaki yanda shugaban kasa Muhammadu Buhari da kan sa ya je wajen yaran nan ya yi mu su jawabi da ba su kwarin guiwa cewa su cigaba da karatun su, kar su bari barazanar wasu miyagun iri ta firgita su, su daina yin kwazo. Zai yi wuya ainun wadannan yara su ga kwamishinan ilimi na Katsina ko ma Gwamna a bulus har ma da yi mu su jawabi in ba irin wannan akasi a ka samu ba. Wannan ya nuna daliban nan da su ka sadaukar da rayuwar su wajen karatun Boko har a ka sace su, sun shiga cikin tarihi da ba za a taba mantuwa da su ba. Daliban sakandaren Kankara 344 sun zama fitattu kuma ko ma Allah ya hukunta wani daga cikin su, zai yi fice nan gaba a duniya ya samu wani babban mukami a cikin Najeriya ko a ketare, to tarihin sa ba zai cika ba sai ya ambaci cewa miyagun iri sun taba sace shi har a ka so fidda rai amma Allah ya hukunta da sauran rabo a rayuwa.Ba na yi wa kowa fatar a sace shi, amma rayuwa ta na da sababi da dalilan da kan daga darajar mutum ko zubar da shi tamkar rugujewar tsaunin kumfa. Tun 1993 in ban manta ba na yi wasu baituka da na ke cewa “tsaunin kumfa taron banza dan yayyafi ka rusawa…” Me zai hana sauran daliban makarantu na firamare da sakandare a inda ba fitina su dage da yin wani abu mai muhimmanci da amfani ga kasa da zai sa akalla shugaban karamar hukumar su ko mai Martaba Sarki ya kai ziyara don yaba mu su. Gaskiya in yaro bai bata hankalin dare ba, to zai yi wuya ya yi suna. Da fatan kuma sunan ya samu da tafarki mai kyau da zai yi amfani al’umma.Ba zan rufe batun nan ba tare da ambatar alwashin babban sufeton ‘yan sandan Najeriya Muhammadu Adamu da ya ba da umurnin daukar matakan kare dukkanin makarantu ko cibiyoyin ilimi a Najeriya daga masu satar mutane. Wannan ma ya faru albarkacin sace daliban makarantar sakandaren Kankara. Zan koma gefe na sha Kankara na jira ganin tabbatar wannan alwashin da irin sa kan taso ne bayan aukuwar wani akasi.

Be the first to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published.


*