25
Jan
Daga jaridar Manhaja Kwamishinoni masu wakiltar jihohi 36 na kasar nan hada da birnin tarayya Abuja, tare da Hukumar Kyautata Da'ar Ma'aikata ta Kasa (FCC) sun rubuta takardar korafi a kan shugabar hukumar FCC Dr. Muheeba Fraida Dankaka zuwa ga Hukumar Yaki da Rashawa da Laifuka Masu Alaka da Rashawa (ICPC) bisa zarginta da yin ba daidai ba da matsayinta. Takardar korafin mai dauke da kwanan wata 18/1/2021 wadda ta sami sa hannun Sir Augustine Wokocha da Abdul Wasiu Bawa-Allah, ta nuna yadda shugabar FCC ta mamaye komai na hukumar sannan ta karbe ayyukan kwamishinonin tana mika wa daraktocinta tare…
