FCMB ya matse kaimi wajen tallafa wa kananan ‘yan kasuwa

Daga jaridar Manhaja

Kawo yanzu, bankin FCMB ya ci gaba da kokarin da yake yi na tallafa wa kanana da matsakaitan ‘yan kasuwa a fadin kasa.

Idan dai za a iya tunawa, a kwanan nan ne aka zabi bakin FCMB a matsayin bakin da ya zarce kowane bakin a yankin Afirka mu’amala da ‘yan kasuwa kanana da matsakaitansu.

Lamarin da ya karfafa wa bankin gwiwa wajen tallafa wa mata masu kananan sana’o’i ta hanyar shirin nan nasa mai taken “SheVenture”.

Shirin SheVenture, shiri ne da bankin ya samar don bunkasa kananan ‘yan kasuwa mata da kuma masu shirin soma kasuwanci, inda yankan ba su rancen kudi mara ruwa da kuma horar da su dabarun kasuwanci.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *