
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Sanannen malamin addinin Musulunci, Sheikh Ahmad Gumi, ya ƙalubalanci dalilin da ya sa babu wani jami’in gwamnati da ya taɓa ziyartar jagorancin ƙungiyar Boko Haram da ‘yan bindiga a hukumance domin tattaunawa akan kawo ƙarshen ayyukan ta’addanci a sassan Nijeriya, yana mai cewa jagororin gwamnatoci a baya sun yi amfani irin salon wajen warware matsalolin rikicin ‘yan yankin Neja-Delta.
Sheikh Gumi ya bayyana haka ne a wani rubutu da aka ɗauko daga shafinsa na Facebook a ranar Asabar, inda ya kamanta salon gwamnatin da al’amarin rashin tsaro na Arewa, yana mai cewa tsohon shugaban ƙasa Goodluck Ebele Jonathan da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Farfesa Yemi Osinbajo sun gabatar da tsarin tattaunawa da mayaƙan Neja-Delta kuma sun yi nasara.
Malamin ya tunatar da cewa, Jonathan da Osinbajo a lokuta mabambanta sun yi ta zuwa domin ganawa da jagororin mayaƙan, a matsayin wani ɓangare na samar da zaman lafiya da wasu shirye-shirye da suka taimaka wajen daƙile ayyukan ta’addanci a yankin mai albarkatun mai.
Ya yi ƙalubalen cewa, mai ya sa ba za a yi amfani da irin salon ba wajan magance matsalolin mayaƙan Boko Haram da ‘yan bindiga da ke addabar sassan arewacin Nijeriya, yana mai cewa duk wanda ya yi yunƙurin bin irin salon sai ya haɗu da suka da cece-kuce daga ɓangaren al’ummar ƙasa.
A tsawon shekaru, Gumi na ɗaukar kansa a matsayin mai kira da a yi amfani da salon tattaunawa da ‘yan bindiga musamman a shiyyar Arewa ta Yamma da ta Gabas wajen magance matsalolin taɓarɓarewar ayyukan ta’addanci.
Akan haka, ya yi ta ƙoƙarin ziyartar sansanonin ‘yan bindiga a Jihar Zamfara da wasu jihohi, yana mai cewa yana yin haka ne domin jin matsalolinsu da kuma kiran a zauna lafiya ta yadda al’umma za su cigaba da rayuwa cikin aminci.
