Rufe mashigar ruwa ta Hormuz ya sake tayar da hankulan masana kan irin raunin da tsarin makamashin Afirka ke da shi, bayan haɗuwa da tasgaro a safarar mai da ya bayyana yadda ƙasashen nahiyar ke ci gaba da dogaro da ƙasashen Asiya da Gabas ta Tsakiya wajen biyan bukatunsu na makamashi.
Wani rahoto da shafin Oil.com ya wallafa ya ce ci gaba da takaita zirga-zirgar jiragen dakon makamashi ta mashigar Hormuz na iya sauya alƙiblar hulɗar makamashi a nahiyar, inda ake hasashen ƙasashe irin su Rasha da Turkiyya za su ƙara faɗaɗa alaƙarsu da gwamnatocin Afirka.
Rahoton ya ce ƙasashen biyu sun riga sun kafa tubalin wannan alaka ta hanyar yarjejeniyoyin tsaro, hadin gwiwar soja da kuma huldar diflomasiyya a wasu sassan nahiyar.
A cewar rahoton, ƙarancin man fetur da takin zamani da ake fuskanta a wasu ƙasashen Afirka ya sake nuna buƙatar gaggauta bunƙasa samar da makamashi a cikin gida da kuma karfafa hanyoyin samar da kayayyaki tsakanin ƙasashen nahiyar.
Sai dai ya nuna cewa Najeriya na daga cikin ƙasashen da suka fara ɗaukar matakan rage dogaro da makamashin da ake shigowa da shi daga ketare ta hanyar bunƙasa hanyoyin samar da makamashi da kuma ƙara ƙarfin tace danyen mai a cikin gida.
Rahoton ya ce idan ƙasashe irin su Najeriya da Angola suka ci gaba da faɗaɗa matatun mai, hakan ba wai kawai zai rage dogaro da tataccen man da ake shigowa da shi ba, har ma zai ƙara wa albarkatun mai darajar tattalin arziki tare da inganta tsaron makamashi a nahiyar.
Masaniyar harkokin kasa da kasa da ke Afirka ta Kudu, Aaliyah Vayez, ta ce rikicin Hormuz ya sake bayyana yadda makomar tattalin arzikin Afirka ke da alaka kai tsaye da sauye-sauyen da ke faruwa a duniya.
Ta ce, “Rikicin Hormuz ya nuna yadda tattalin arzikin Afirka ke haɗe da tsarin tattalin arzikin duniya. Wannan ya ƙara nuna muhimmancin ƙasashen nahiyar su gina ƙarfin cikin gida, su faɗaɗa hadin gwiwa da sauran ƙasashe, sannan su rage raunin da suke da shi a ɓangarorin makamashi, kasuwanci da hanyoyin samar da kayayyaki.”
