Houthi ta sauya akalar safarar man Saudiyya yayin da yaƙin Amurka da Iran ke ƙara tsananta

Spread the love

Rikicin da ke tsakanin Amurka da Iran ya sake ɗaukar sabon salo bayan ƙungiyar Houthi ta Yemen ta buɗe wani sabon fagen matsin lamba ta hanyar kakaba takunkumin ruwa kan Saudiyya, matakin da ya fara girgiza harkokin safarar mai da zirga-zirgar jiragen ruwa a yankin Gabas ta Tsakiya.

Sabon matakin ya tilasta wasu manyan jiragen dakon danyen man Saudiyya guda biyu da suka nufi kasuwannin Chana da Indiya sauya alkibla a Tekun Bahar Maliya, domin kauce wa mashigin Bab el-Mandeb bayan Houthi ta yi barazanar kai hari kan duk wani jirgin da zai dauki ko sauke man Saudiyya.

Masana harkokin tsaron teku sun ce wannan shi ne karon farko da aka tabbatar jiragen kasuwanci sun sauya hanyarsu saboda sabon takunkumin Houthi, lamarin da ke nuna rikicin ya fara shafar cinikayyar duniya kai tsaye.

Wannan na faruwa ne a daidai lokacin da hare-haren da ɓangarorin biyu ke kai wa juna suka kara tsananta. Dakarun Amurka sun sake kai hare-hare kan cibiyoyin sojin Iran da wuraren harba makamai masu linzami da jiragen sama marasa matuki a kudanci da yammacin ƙasar, yayin da Iran ta mayar da martani da hare-hare kan wuraren da ke da alaka da Amurka a Bahrain, Kuwait da Jordan.

Iran ta kuma ce ta kai hari kan wasu muhimman kayayyakin more rayuwa a Bahrain, ciki har da cibiyar adana bayanai da kamfanin Amazon ke gudanarwa, ko da yake har zuwa lokacin hada wannan rahoto ba a samu tabbatar da hakan daga ɓangaren kamfanin ba.

A gefe guda, hukumomin tsaron teku sun ce wani jirgin dakon mai ya gamu da hari a mashigin Hormuz, yayin da Iran ta ce wasu jiragen dakon mai biyu sun kama da wuta bayan fashewar abubuwa yayin ƙoƙarin ketare mashigin.

Rikicin ya ƙara jefa duniya cikin fargaba saboda mashigun Hormuz da Bab el-Mandeb na daga cikin hanyoyin da suka fi muhimmanci wajen jigilar danyen mai. Bayan zirga-zirga ta ragu a Hormuz sakamakon yakin, Bahar Maliya ta zama babbar hanyar da Saudiyya ke amfani da ita wajen fitar da man fetur zuwa kasuwannin duniya. Sai dai barazanar Houthi na iya kawo cikas ga wannan hanya ma.

Tasirin hakan ya fara bayyana a kasuwannin duniya, inda farashin danyen mai na Brent ya haura dala 91 kan ganga, yayin da farashin man fetur a Amurka ya sake haura dala hudu kan galan.

By ukarofi

Leave a Reply