Cutar Ebola: Hukumar CDC ta Afirka ta buƙaci Amurka ta janye takunkumin tafiye-tafiye kan Uganda

Spread the love

Babban daraktan Hukumar Yaki da Cututtuka ta Afirka (Africa CDC), Jean Kaseya, ya buƙaci gwamnatin Amurka da ta janye takunkumin tafiye-tafiye da ta kakaɓa wa Uganda sakamakon ɓarkewar cutar Ebola, yana mai cewa babu wani dalili da zai sa a ci gaba da ɗaukar irin wannan mataki bayan ƙasar ta shafe kusan wata guda ba tare da samun sabon mai ɗauke da cutar ba.

Kaseya ya bayyana hakan ne a wani taro da aka gudanar a Accra, babban birnin Ghana, inda ya ce ya aike wa Sakataren Lafiya na Amurka, Robert F. Kennedy Jr., wasiƙa yana rokon a soke takunkumin.

Ya kuma yi kira ga ƙasashen Afirka su mara wa wannan buƙata baya domin nuna hadin kan nahiyar ga ƙasashen da cutar Ebola ta shafa, musamman Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo, wadda har yanzu ita ce cibiyar ɓarkewar cutar.

A cewarsa, Uganda ta samu ci gaba sosai wajen daƙile yaɗuwar Ebola. An sallami mara lafiyarta na ƙarshe daga asibiti a ranar 16 ga Yuli, lamarin da ya fara ƙirga kwanaki 42 da Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta tanada kafin a ayyana wata ƙasa ta kuɓuta daga cutar idan ba a sake samun sabon kamuwa ba.

Ya zuwa yanzu Uganda ta tabbatar da mutum 20 da suka kamu da Ebola, adadi mai nisa da na Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo, inda aka samu sama da mutum 2,400 da suka kamu da cutar.

By ukarofi

Leave a Reply