Mutane 144 sun mutu a tekun Mauritania yayin ƙoƙarin tsallakawa Turai

Spread the love

Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (UNHCR) ta ce akalla mutum 144 ne aka tabbatar sun mutu ko kuma suka ɓace a gabar tekun Mauritania yayin da suke ƙoƙarin tsallakawa zuwa Turai ta ruwa.

A cewar hukumar, adadin ya biyo bayan wasu ayyukan ceto uku da aka gudanar tsakanin 14 zuwa 18 ga Yuli, inda aka kuɓutar da daruruwan mutane daga jiragen da suka shiga mawuyacin hali a teku.

Mummunan haɗarin ya fi shafar wani jirgin ruwa da ya tashi daga Bufaloto a ƙasar Gambia. Jirgin ya shafe kwanaki 25 yana yawo a teku kafin a ceto shi a ranar 18 ga Yuli. Lokacin da ya isa Mauritania, yana ɗauke da gawawwaki masu yawa, yayin da mutum 38 kacal suka tsira.

Hukumar ta bayyana cewa cikin waɗanda suka tsira akwai ƙananan yara biyu da suka rasa dukkan iyalansu a wannan tafiya. A halin yanzu suna karɓar kulawa a asibiti, yayin da ba a tabbatar ko yawancin waɗanda suka mutu sun nutse ne ko kuma yunwa, kishirwa ko wasu matsaloli ne suka yi sanadin rasuwarsu ba.

UNHCR ta ce dukkan wadanda abin ya shafa sun fito ne daga ƙasashen da ke kudancin hamadar Sahara, kuma tsakanin 14 zuwa 18 ga Yuli an ceto mutum 387 a ayyukan ceto uku da aka gudanar a gabar Mauritania.

Tun daga farkon shekarar 2026, an ceto mutum 2,147 bayan jiragensu sun sauka ko suka isa tashoshin Nouadhibou da Nouakchott a Mauritania.

By ukarofi

Leave a Reply