Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Wasu da ake zargin ’yan bindiga ne sun sace ƙanin ɗan Majalisar Dokokin Jihar Kaduna mai wakiltar Mazabar Kubau, Hon. Shehu Pambegua, a gidansa da ke garin Pambegua, ƙaramar Hukumar Kubau ta jihar.
Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 10 na daren ranar Litinin, lokacin da ’yan bindigar suka je da wata mota kirar Sharon, suka mamaye gidan ɗan majalisar tare da yin awon gaba da ƙaninsa mai suna Sunusi.
Da yake tabbatar da harin a cikin wata sanarwa, Kakakin Hukumar Tsaro ta Jihar Kaduna (KADVIS), Yunusa Shehu Ibrahim, ya ce harin ya faru ne sa’o’i kaɗan bayan kashe jami’an KADVIS uku da wasu da ake zargin ’yan bindiga ne suka yi a kan hanyar Zariya zuwa Pambegua, a ƙaramar Hukumar Kubau.
Sanarwar ta bayyana sunayen jami’an da aka kashe da cewa su ne Damlami Dantani, Mataimakin Shugaban KADVIS na Biyu (2IC) a ƙaramar Hukumar Kubau, Abdullahi Hamisu da kuma Zakariyya Musa.
Ta ce jami’an suna gudanar da sintirin tsaro na yau da kullum ne a lokacin da suka yi ƙoƙarin tsayar da wata mota kirar Volkswagen Golf mai launin ja, amma ta ƙi tsayawa.
Hakan ya sa jami’an suka bi motar da motar sintiri ta hukumar domin tabbatar da mutanen da ke cikinta da kuma dalilin tafiyarsu.
Daga bisani, waɗanda ake zargin suka buɗe wa jami’an da ke bin su wuta, inda suka kashe Mataimakin Shugaban KADVIS na Biyu, Danlami Dantani.
Ibrahim ya ƙara da cewa daga baya maharan sun juya suka nufi ofishin KADVIS, inda suka sake buɗe wuta tare da raunata Abdullahi Hamisu da Zakariyya Musa, waɗanda daga bisani suka rasu sakamakon raunukan da suka samu.
Daga nan ne maharan suka tsere ta hanyar Zariya.
Da yake martani kan lamarin, Kwamandan KADVIS na Jihar Kaduna, Ali D. Audu, ya jajanta wa iyalan jami’an da suka rasa rayukansu, yana mai bayyana mutuwarsu a matsayin babban rashi ga hukumar da Jihar Kaduna baki ɗaya.
Sai dai ya yaba wa jami’an da suka rasu bisa jajircewarsu da sadaukar da kai wajen gudanar da ayyukansu, tare da tabbatar wa iyalansu cewa ba za a manta da irin sadaukarwar da suka yi ba.
Kwamandan ya kuma tabbatar da cewa jami’an tsaro sun ƙara tsaurara matakan tsaro a garin Pambegua da kewaye, yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin ceto Sunusi da kuma cafke waɗanda suka aikata laifin.
Audu ya kuma yi kira ga jami’an KADVIS da su ci gaba da kasancewa cikin shiri tare da aiki kafada da kafada da sauran hukumomin tsaro domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma a faɗin Jihar Kaduna.
