‘Yan kasuwa fiye da 450 suka amfana da jari a Bichi

Spread the love

Ƙungiyar kasuwar zamani ta Bichi sun jinjina wa shugaban hukumar kula da ƙananan sana’o’i da tallace-tallace na jihar Kano.

Kamar yadda jami’ar yaɗa labarai ta ƙaramar hukumar Bichi, Jamila Abdullahi Rijiyar Lemo ta rawaito, ƙungiyar ta kai ziyarar girmamawa ga shugaban hukumar kula da ƙananan sana’o’i da tallace-tallace ta Jihar Kano, Alhaji Abubakar Ahmad Bichi, a ofishinsa da ke cikin birnin Kano.

A yayin ziyarar, an tattauna muhimman batutuwan da suka shafi cigaba da ƙarfafa ‘yan kasuwa, musamman samar da jari ga ƙananan ’yan kasuwa da samar da guraben koyar da sana’o’i ga matasa maza da mata a ƙaramar hukumar Bichi.

Shugaban ƙungiyar, Alhaji Abubakar Mazahimu Sale, ya bayyana farin ciki da jin daɗin yadda Alhaji Abubakar Ahmad Bichi, ya tarbe su tare da sauraren buƙatun ’yan kasuwar. Inda ƙungiyar kuma ta yi godiya bisa irin tallafin da suka samu a baya, wanda sama da mutum 250 daga Bichi suka ci gajiyar tallafin naira dubu 50, yayin da sama da mutum 200 suka ci gajiyar tallafin mahauta, ƙarƙashin ofishin Alhaji Abubakar Ahmad Bichi, bisa sahalewar Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf.

A nasa jawabin, Alhaji Abubakar Ahmad Bichi, ya bayyana farin cikinsa da wannan ziyara, tare da alƙawarin yin aiki tuƙuru; kuma kafada da kafada da ƙungiyar ‘yan kasuwar domin ƙara samar da cigaba da bunƙasa tattalin arzikin ƙaramar hukumar Bichi.

Shi kuwa sarkin kasuwar zamanin, Malam Muhammad Shu’aibu Arewa, addu’a da fatan alheri ya yi ga shugaban hukumar, yayin da Alhaji Murtala Hashim ya jaddada muhimmancin kula da ƙananan ’yan kasuwa gami da samar musu tallafi, duba da irin yadda suke taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa tattalin arzikin al’umma baki ɗaya.

A ƙarshe, mataimakin shugaban ƙungiyar, Sabo Idris, ya yi matuƙar jinjina ga shugaban hukumar a madadin dukkan ‘ya’yan ƙungiyar, bisa kyakkyawan ƙudirinsa na haɗa gwiwa da ’yan Kasuwar zamanin ta Bichi.

By ukarofi