Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Tsohon Gwamnan Jihar Ekiti kuma tsohon Ministan Ma’adinan ƙasa, Kayode Fayemi, ya bayyana alkawarin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, na dawo da tallafin man fetur a matsayin dabarar siyasa ta neman ƙuri’u, ba manufar tattalin arziki ba.
Fayemi ya kwatanta matakin Atiku da tikitin Muslim-Muslim da jam’iyyar APC ta yi amfani da shi a zaɓen shugaban ƙasa na 2023, yana mai cewa alkawarin dawo da tallafin zai iya samun karɓuwa musamman daga ’yan Nijeriya masu ƙaramin ƙarfi da cire tallafin ya fi shafa.
Ya bayyana hakan ne a wata hira da shirin Prime Time na Arise Teleɓision ranar Litinin.
Fayemi ya ce alkawarin dawo da tallafin man fetur na iya jan hankalin ’yan Nijeriya da ke fama da tsadar rayuwa, musamman masu ƙaramin ƙarfi.
Sai dai ya sake jaddada cewa yana goyon bayan cire tallafin man fetur, yana mai cewa ya daɗe yana fafutukar ganin an cire shi tun lokacin da yake Shugaban ƙungiyar Gwamnonin Nijeriya.
A cewarsa, Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya gaji wani aiki da gwamnatin da ta gabata ta riga ta kammala kan batun cire tallafin, amma ya ce matsalar ita ce yadda aka aiwatar da manufar.
Fayemi ya kuma bayyana cewa tun kafin cire tallafin, gwamnonin jihohi sun yi aiki tare da gwamnatin tarayya da Bankin Duniya wajen samar da wani tsarin tallafa wa masu ƙaramin ƙarfi, domin rage musu radadin tasirin cire tallafin.
Ya ce Atiku na amfani da wahalhalun tattalin arzikin da ’yan Nijeriya masu ƙaramin ƙarfi ke fuskanta wajen neman samun goyon bayan jama’a, ta hanyar alkawarin dawo da tallafin man fetur.
Fayemi ya ce yawancin ’yan Nijeriya ba sa mayar da hankali sosai kan muhawarar tattalin arzikin da ake yi kan tallafin, illa dai suna son samun damar biyan bukatun yau da kullum, ciyar da iyalansu da kuma tura ’ya’yansu makaranta.
Ya kuma danganta talauci da rashin daidaito da matsalar tsaro, yana mai cewa matsin tattalin arziki na daga cikin abubuwan da ke taimakawa wajen ci gaba da samun ayyukan ’yan ta’adda da ’yan bindiga a Nijeriya.
