Gwamnatin Filato ta umarci a buɗe makarantu a gobe Litinin duk da fargabar annobar mashaƙo

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamnatin Jihar Filato ta umarci a sake buɗe baki ɗaya makarantun firamare da sakandare na gwamnati a sassan jihar daga Litinin, 14 ga Satumba, 2026, bayan aiwatar da matakan kariya na daƙile cigaba da yaɗuwar cutar mashaƙo da ta ɓarke a wasu ƙananan hukumomin jihar.

Ta ce, hakan na da nufin daidaita buƙatar bayar da kariya ga ɗalibai, malamai da sauran ma’aikatan makarantu tare da buƙatar tabbatar da cigaba da gudanar da harkokin karatu. Hakan na zuwa ne bayan rufe makarantun na wucin-gadi a ‘yan kwanakin da suka gabata domin samun damar daƙile yaɗuwar cutar a sauran sassan jihar.

A ranar 7 ga Satumba rufewar ta fara aiki, inda gwamnatin ta ce ta yi hakan ne da nufin ɗaukar matakin kariya da zai bai wa hukumomin lafiya damar gano ainihin halin al’amarin da ƙarfafa sanya ido a kai da kuma ƙoƙarin ɗaukar matakan da suka dace ga yankunan da annobar ta afka wa.

A wata sanarwa da ke ɗauke da sanya hannun Kwamishinar Yaɗa Labaran jihar Joyce Ramnap, gwamnatin ta tabbatar wa iyaye da jagororin makarantu cewa an ɗauki matakan lafiya na taƙaice matakin yaɗuwar cutar yayin da aka sake buɗe makarantu.

Akan haka ne kuma gwamnatin ta umarci hukumomin makarantu da malamai da su kula da tsaftace muhallansu da ɗaukar matakan kariya yayin da suka gano wani abu tare da sanya ido kan alamun samuwar cutar mashaƙo gami da gaggauta ruwaito wa hukumomin lafiya.

By Babaji

Leave a Reply