Gwamnonin Arewa sun yi jimamin rasuwar tsohon shugaban PDP tsohon gwamnan Gongola, Bamanga Tukur

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Arewacin Nijeriya (NNGF) kuma Gwamnan Jihar Gombe, Inuwa Yahaya, CON, ya bayyana kaɗuwarsa kan rasuwar ɗaya daga cikin manyan ƙasa, tsohon Gwamnan tsohuwar Jihar Gongola kuma tsohon Shugaban Jam’iyyar PDP, Alhaji Bamanga Tukur (Tafidan Adamawa).

Marigayi Bamanga Tukur ya rasu ne a Abuja a ranar Asabar, 12 ga Satumba, 2026, kamar yadda rahotanni suka bayyana.

A wani saƙon ta’aziyya da ya fitar a madadin takwarorinsa na NNGF, Gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana rasuwar tsohon dattijon ƙasar a matsayin babban rashi ga arewacin Nijeriya da ma ƙasar baki ɗaya. Ya ce, Nijeriya ta rasa ɗaya daga cikin mafiya ƙwarewar aikin gwamnati, jagororin siyasa kuma jiga-jigan ci-gaban harkar tattali.

A cikin saƙon, wanda ke ɗauke da sanya hannun Sakataren Harkokin Yaɗa Labaran gwamnatin Gombe, Isma’ila Uba Misilli, Gwamna Yahaya ya ce hidimar Bamanga Tukur ga ƙasa ta shafe tsawon sama da shekaru 60. A lokacin ya riƙe muƙamai daban-daban ciki har da Shugaban Hukumar kula da Tashoshin Jiragen Ruwa NPA, Gwamnan Gongola da Ministan Masana’antun Jihar.

Shugaban na NNGF ya kuma tunatar da gudumawar marigayin a cigaba tattalin arziƙin Afirka ta shirin Africa Business Roundtable da kamfanin NEPAD Business Group da kuma jagorancin PDP a matsayin shugaba daga 2012 zuwa 2014.

Gwamna Inuwa Yahaya ya ce, ƙwarewar marigayin a fannin gudanarwar harkokin gwamnati, siyasa, kasuwanci da lamuran nahiya sun sa shi yin fice cikin zamaninsa, wanda gudunmawar za ta cigaba da kasancewa a tarihin Nijeriya.

A ƙarshe, gwamnan ya yi wa gwamnati da al’ummar Adamawa, iyalan Bamanga Tukur da abokan arziƙi jajen rashin, yana mai addu’ar Allah ya jiƙan sa ya kuma gafarta masa kurakuransa da kuma saka masa da gidan Aljannatul Firdausi.

By Babaji

Leave a Reply