Ambaliya: Gwamnatin Neja ta ja hankalin al’ummar da ke yankunan Kogin Kaduna kan buɗe madatsar Shiroro

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamnatin Jihar Neja ta fitar da sanarwar gargaɗi ga mazauna da ƙauyukan da ke kusa babban kogin Kaduna kan ƙaruwar matakan ruwa a madatsar ruwa ta Shiroro yayin daminan 2026.

Ta ce, akwai yiwuwar a riƙa buɗe madatsar lokaci bayan lokaci yayin daminar bana domin tabbatar da aminci ga tsarinta tare da ƙoƙarin bayar da kariya ga ƙauyukan da ke kewayen kogin.

Wannan gargaɗi na ƙunshe ne a cikin wata takarda da Kwamishinan Yaɗa Labaran jihar, Obed Nana ya fitar a ranar Juma’a a Minna. Ya bayyana cewa, an fitar da saƙon ankararwar ne bayan samun wata sanarwa daga Kamfanin North South Company Ltd (NSPCL), reshen gudanarwa na tashar lantarkin Shiroro, wadda ke nuna an samu ƙarin matakin ruwa a rafin na Kaduna da madatsar Shiroro.

A cewarsa, abin da kamfanin ya gano ya nuna cewa za a cigaba da samun hauhawar ruwa yayin da daminar 2026 ke wakana, wanda kuma ya yi daidai da hasashen Hukumar kula sa Yanayi ta Ƙasa, NiMet.

Ya bayyana cewa, sako ruwan da za a yi idan an samu buƙatar haka, zai zama matakin kariya na bunƙasa tsaron tsarin madatsar da kare ƙauyukan al’ummar da ke yankinta.

Akan haka ne kwamishinan ya yi kira ga mazauna da su kasance masu lura da zama a ankare har zuwa ƙarshen damina, musamman waɗanda suke yankuna masu barazanar ambaliya.

By Babaji

Leave a Reply