Gwamnatin Tarayya ta bada tabbacin aminci yayin koma wa makarantun Unity a Litinin

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ministan Ilimi, Dakta Maruf Tunji Alausa, ya ce kasantuwar aminci da zaman lafiyar ɗalibai da ma’aikata sune ababen da Gwamnatin Tarayya take fifitawa. Alausa ya bayyana cewa, an sanar da hukumomin masu ruwa da tsaki shirin koma wa karatu a makarantun haɗaka na kwalejojin tarayya, wato Federal Unity Schools, yayin da ta buƙaci su ƙarfafa matakan tsaro aciki da kewayensu.

A cewarsa, an ɗauki matakan tsaron ne da nufin bayar da kariya ga ɗalibai, ma’aikata da kuma al’ummar da ke kewayen makarantun yayin da ake shirin koma wa aiki acikinsu a sassan ƙasar.

Ministan ya kuma kirayi iyaye da wakilansu da su kwantar da hankali tare da zama masu dogara da bayanan da ake fitarwa a hukumance wajen shirya wa komawar ‘ya’yansu makaranta a ranar Litinin, 14 ga Satumba, 2026. Haka kuma, ya umarci kwalejojin da su bayar da cikakken haɗin kai ga hukumomin tsaro da sauran hukumomi domin tabbatar da komawar bisa tsari da aminci.

Sannan, Alausa ya yi kira ga ɗalibai, iyaye, malamai da mahukuntan makarantun da sauran masu ruwa da tsaki da su yi aiki tare wajen tafiyar da yanayin walwalar makarantu da kewayensu kan tsari, yana mai cewa alhaki ne akan kowane mai ruwa da tsaki bayar da kariya ga ɗalibai.

Kazalika, ma’aikatar ta ce za ta cigaba da sanya ido kan halin da ake ciki da ɗaukar matakan da suka dace don ganin an koma bakin aiki cikin aminci tare da tabbatar da ɗorewarsa. Hakan na zuwa ne yayin da al’umma suke kokawa kan halin tsaro da yadda ake gudanar da al’amura a wasu sassan makarantun.

By Babaji

Leave a Reply