JIPHARMA: Jigawa za ta fara ƙera magungunan asibiti

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Gwamnatin Jihar Jigawa ta fara shirin sauya Kamfanin Hada-Hadar Magunguna na Jihar (JIPHARMA) daga kamfanin da ke sayar da magunguna zuwa kamfanin da zai riƙa kera magunguna.

Gwamna Umar Namadi ne ya bayyana hakan yayin bikin rantsar da sabuwar Hukumar Gudanarwar JIPHARMA.

Ya ce matakin na daga cikin ƙoƙarin gwamnatinsa na sake fasalin kamfanonin gwamnati domin su kasance masu inganci da dorewa, tare da bayar da gudunmawa wajen bunƙasa tattalin arzikin jihar.

Gwamnan ya bayyana cewa gwamnati ta riga ta samu shawarwari daga wasu masu zuba jari da ke sha’awar shiga harkokin kamfanin ta hanyar tsarin haɗin gwiwar gwamnati da ’yan kasuwa, wato PPP.

Sai dai ya ce gwamnatin za ta yi nazari mai zurfi kan duk wata yarjejeniya da za a ƙulla da masu zuba jari, domin tabbatar da cewa ba ta tauye haƙƙin al’ummar Jigawa ba.

Ya ce: “A gare mu, yana da muhimmanci a yi la’akari da irin wannan yarjejeniya a hankali, sannan a tsara ta ta yadda za ta amfani al’ummar Jigawa.”

Gwamna Namadi ya ce an zaɓi mambobin sabuwar hukumar ne bisa la’akari da ƙwarewarsu, tarihin ayyukansu da kuma amincinsu.

Ya ce irin waɗannan siffofi za su taimaka wajen tabbatar da kyakkyawan shugabanci yayin da JIPHARMA ke shirin sauya salon gudanar da ayyukanta.

Gwamnan ya ce yana da yaƙinin cewa hukumar za ta iya jagorantar kamfanin daga harkar sayar da magunguna zuwa matakin kera magunguna da kansa.

Ya kuma yaba wa Shugaban Hukumar, Pharm. Hashim Ubale Yusufu, bisa alkawarin da ya yi na tabbatar da bin ƙa’idojin ɗa’a, gaskiya da kuma riƙon amana wajen gudanar da kamfanin.

Gwamna Namadi ya ce wannan alkawari, tare da ƙwarewar sauran mambobin hukumar, ya ƙara masa ƙwarin gwiwar cewa JIPHARMA na da damar samun nasarar wannan sauyi.

Gwamnan ya buƙaci hukumar da ta yi amfani da ƙwarewarta wajen sake fasalin kamfanin, tare da tabbatar da kyakkyawan tsarin tafiyar da shi, gaskiya da kuma riƙon amana.

Ya kuma jaddada muhimmancin samar da kyakkyawan tsarin haɗin gwiwa tsakanin JIPHARMA da masu zuba jari da sauran abokan hulɗa.

A cewarsa, irin wannan haɗin gwiwa zai taimaka wajen mayar da kamfanin zuwa wata babbar cibiyar samar da magunguna mai ɗorewa.

Ya ce aikin da ke gaban hukumar gagarumi ne, amma yana da ƙwarin gwiwar cewa idan aka haɗa ƙwarewar ƙwararru, shugabanci nagari da kuma zuba jari mai ma’ana, JIPHARMA za ta iya zama kamfanin kera magunguna mai ƙarfi.

Idan shirin ya yi nasara, ana sa ran zai taimaka wajen inganta samar da magunguna a Jigawa, samar da guraben zuba jari, da kuma ƙara sauƙaƙa samun magunguna da sauran kayayyakin kiwon lafiya ga al’ummar jihar da ma sauran sassan Nijeriya.

Gwamna Namadi ya kuma yi wa mambobin sabuwar hukumar addu’ar samun jagorancin Allah da kariya, tare da fatan samun nasara wajen gudanar da aikin da aka ɗora musu.

By ukarofi