
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Kakakin Majalisar Wakilai Tajudeen Abbas, ya yi kira da a riƙa ɗaukar matakai masu tsauri akan masu safarar miyagun ƙwayoyi da ƙara matakin bayar da tallafi ga waɗanda suke fama da matsalolin shaye-shaye, yana mai cewa yawan amfani da miyagun ƙwayoyi na barazana ga zaman lafiyar al’umma.
Wajibi ne mu hukunta waɗanda suke ribata daga ƙwayoyi. Wajibi ne mu yi magani ga waɗanda suka zama ‘yan ƙwaya. Dilan yana buƙatar doka. Wanda ya dogara kuma yana buƙatar kulawa,” inji Abbas.
Ya kuma ce, yayin da akwai gwamnati, dole a samu doka tana aiki tare da damawa da al’umma ta yadda za a shawo kan matsalolin safarar ƙwayoyi da amfani da su acikin al’umma. Kakakin ya bayyana haka ne a ranar Asabar, yayin rufe taron kwana uku akan amfani da ƙwayoyi ba bisa ƙa’ida ba da rikice-rikicen cikin gida a Jihar Kaduna.
An gudanar da shirin ne bisa haɗin-gwiwar Hukumar Wayar da Kai ta Ƙasa (NOA), wanda ya shafi mazaɓar shugaban majalisar. Ya bayyana cewa, magance matsalolin harkar ƙwaya acikin al’umma na buƙatar aiki kafaɗa-da-kafaɗa wanda ya haɗa da cikin iyalai, makarantu, yankuna da hukumomin tabbatar da biyayya ga dokokin ƙasa, yana mai cewa wajibi ne a riƙa lura da sauye-sauye na lokaci guda a harkar zamantakewa.
Sannan su ma makarantu su samar da tsarin faɗakarwa da ruwaito alamun farko na shiga harkar shaye-shayen ƙwayoyi ba bisa doka ba kamar yadda ya zama wajibi shagunan siyar da magani su guji siyarwa ba tare da kulawa ba, kamar yadda kakakin ya bayyana.
Kazalika, Tajudeen Abbas ya ce wajibi ne jagororin al’umma da suka haɗa da masu muƙaman sarauta da na addini su yaƙi harkar shaye-shaye acikin al’ummarsu da ƙoƙarin ruwaito wa hukumomi dukkan wani zargin zirga-zirgar miyagun ƙwayoyi da suka gano a yankunansu.
