2027: Yari ya gana da malaman Musulunci na Zamfara akan Tinubu

Spread the love

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Sanata Abdulaziz Yari, tsohon gwamnan jihar Zamfara, kuma babban darakta na kwamitin yaƙin neman zaɓen shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a yau Asabar ya gana da tawagar malaman Musulunci a jihar Zamfara domin neman taimakon Allah don samun zaman lafiya mai ɗorewa a Najeriya da kuma goyon bayan Shugaba Bola Ahmed Tinubu kafin babban zaɓen 2027.

A lokacin taron da aka gudanar a gidansa da ke garin Talata Mafara, Sanata Yari ya jaddada rawar da malaman addinin ke takawa wajen zaman lafiyar ƙasa.

Ya yi kira ga malamai da su ƙara himma wajen addu’o’i don dawo da zaman lafiya da tsaro a faɗin ƙasar, musamman a yankin Arewa maso Yamma.

Ya ce gwamnatin tarayya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Tinubu tana ci gaba da jajircewa wajen magance rashin tsaron da ke addabar al’ummomi a Zamfara da sauran sassan Nijeriya.

“Shugaban ƙasa yana aiki dare da rana don magance rashin tsaro a Arewa maso Yamma da sauran sassan ƙasar,” in ji Yari.

“Muna buƙatar goyon bayan shugabannin addinai don samun nasarar shugaban ƙasa da ƙoƙarin gwamnati ta hanyar addu’o’i da wayar da kan jama’a.” Ya ce

Sanatan ya kuma buƙaci malaman addini da su wayar da kan mabiyansu kan nasarorin da gwamnati mai ci a fannin tattalin arziki da sauran fannoni, yana mai lura da cewa fahimtar da jama’a tana da matuƙar muhimmanci wajen ci gaba da gudanar da tsare tsaren cigaba.

A cikin addu’o’insu daban-daban, malaman addinin Musuluncin sun yi addu’ar samun nasarar yaƙin neman zaɓe cikin lumana da kuma zaɓe mai inganci a shekarar 2027.

Sun yi alƙawarin bada goyon bayansu ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu da gwamnatin tarayya a babban zaɓe mai zuwa.

Malaman sun yaba wa Sanata Yari kan nuna muhimmancin su kuma sun tabbatar masa da ci gaba da jajircewarsu na yin wa’azin haɗin kai, haƙuri, da goyon bayan manufofin gwamnati da nufin inganta walwalar ‘yan ƙasa.

By ukarofi