Rahusar abinci da ayyukan yi talakawan Nijeriya ke buƙata – Oye ga Gwamnatin Tarayya

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Shugaban ƙungiyar Binciken Tattalin Arziki da ɗa’a ta ƙasa, Dele Oye, ya buƙaci Gwamnatin Tarayya ta tabbatar da cewa nasarorin da aka samu a fannin tattalin arziki a baya-bayan nan sun sauya zuwa ingantacciyar rayuwa ga talakawan Nijeriya.

Oye ya amince cewa sauye-sauyen tattalin arzikin da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta aiwatar sun taimaka wajen ƙarfafa daidaiton tattalin arzikin Nijeriya tare da inganta matsayin tattalin arzikin ƙasar baki ɗaya.

An bayyana matsayar tasa ne cikin wata sanarwa mai taken, “Tattalin Arziki Na Daidaituwa, Yanzu A Bari Jama’a Su Ga Amfaninsa,” wadda Oye, shugaban GTE, ya fitar.

Ya jaddada cewa ci gaban tattalin arziki ba zai yi wa ’yan ƙasa ma’ana sosai ba matuƙar bai haifar da raguwar farashin kayan abinci, ƙarin guraben ayyukan yi da ingantacciyar rayuwa ba.

Oye ya ce, Gwamnatin Tarayya ta ɗauki wasu matakai masu tsauri, ciki har da cire tallafin man fetur, sake fasalin kasuwar canjin kuɗin waje, tsaurara manufofin kuɗi da kuma ƙara gina asusun ajiyar kuɗaɗen waje na ƙasar.

A cewarsa, waɗannan matakai sun taimaka wajen magance wasu daga cikin matsalolin tattalin arzikin da suka dade suna raunana tubalin tattalin arzikin Nijeriya.

Ya bayyana cewa asusun ajiyar kuɗaɗen waje na Nijeriya ya ƙaru zuwa dala biliyan 53.11 a ranar 24 ga Agusta, 2026, yana mai cewa hakan na nuna cewa ƙasar ta samu ƙarin ƙarfin kariya daga matsalolin kuɗi.

Oye ya kuma yi nuni da alkaluman ci gaban tattalin arziki na baya-bayan nan da Hukumar ƙididdiga ta ƙasa (NBS) ta fitar, waɗanda suka nuna cewa tattalin arzikin Nijeriya ya bunƙasa da kashi 4.43 cikin 100 a kwata na biyu na shekarar 2026, idan aka kwatanta da kashi 3.89 cikin 100 a kwata na farko.

Ya ce, an samu wannan ci gaba ne a ɓangarorin mai da waɗanda ba na mai ba, lamarin da ke nuna cewa tattalin arzikin ƙasar na fara samun ƙarin kuzari.

Sai dai duk da waɗannan ci gaba, Oye ya yi gargaɗin cewa ƙaruwa da asusun ajiyar kuɗaɗen waje da bunƙasar tattalin arziki ba su isa su tabbatar da ingantacciyar rayuwar ’yan Nijeriya kai tsaye ba.

Ya yi nuni da wani rahoton IMF, wanda ya kiyasta cewa talauci na ci gaba da yin kamari a Nijeriya, yayin da miliyoyin ’yan ƙasa ke fuskantar matsalar rashin isasshen abinci.

A cewarsa, waɗannan alkaluma na nuna babban gibi tsakanin yadda tattalin arzikin ƙasa ke tafiya a takarda da kuma irin halin da iyalai ke fuskanta a rayuwarsu ta yau da kullum.

Saboda haka, Oye ya buƙaci Gwamnatin Tarayya ta bai wa manufofin da za su sa jama’a su fara ganin amfanin sauye-sauyen tattalin arziki a rayuwarsu ta yau da kullum fifiko.

Ya ce ya kamata ’yan Nijeriya su amince da ci gaban da gwamnati ta samu, amma a lokaci guda su ci gaba da buƙatar ɗaukar ƙarin matakai a wuraren da sauye-sauyen tattalin arzikin ba su riga sun haifar da wadata ba.

A cewarsa, sauye-sauyen sun kasance masu wahalar aiwatarwa a fagen siyasa tare da jefa ’yan ƙasa cikin matsin tattalin arziki, amma a gefe guda sun magance wasu matsalolin da suka daɗe suna gurgunta tattalin arzikin ƙasar.

Oye ya ce, yanzu dole ne gwamnati ta wuce matakin daidaita tattalin arziki zuwa ƙirƙirar ayyukan yi masu inganci, rage tsadar rayuwa da tabbatar da cewa ci gaban tattalin arziki yana haifar da sauyi mai ma’ana ga iyalai a faɗin ƙasar.

Ya jaddada cewa daidaiton tattalin arziki mataki ne na farko kawai, inda ya ce ainihin gwajin nasarar sauye-sauyen shi ne irin tasirin da za su yi kan rayuwar talakawan Nijeriya.

Ya buƙaci gwamnati ta sauya abin da ya kira daidaiton tattalin arziki zuwa “tabbacin tsaro a rayuwar yau da kullum”, tare da tabbatar da cewa tattalin arzikin ƙasar ba wai kawai ya zama abin da masu zuba jari za su iya dogaro da shi ba, har ma ya zama mai amfani da sauƙin rayuwa ga iyalai.

By ukarofi

Leave a Reply