2027: Kungiyar Kiristocin Arewa ta buƙaci a ƙara bai wa matasa damar shiga siyasa

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Kungiyar Kiristocin Arewa ta Northern Christian Professionals ta yi kira ga shugabannin siyasa da jam’iyyun siyasa da su ƙara buɗe ƙofa ga matasan Arewa domin su taka rawa a harkokin siyasa da shugabanci, yayin da Nijeriya ke shirin tunkarar babban zaɓen 2027.

Kungiyar, wadda na daga cikin ƙungiyoyin Kiristoci na farko da suka goyi bayan takarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu da Mataimakin Shugaban ƙasa, Kashim Shettima, a zaɓen 2023, ta ce tana ƙoƙarin ƙarfafa haɗin kan masu ruwa da tsaki da kuma samar da ingantacciyar tattaunawa kan makomar siyasar Arewa.

A yayin taron Majalisar Jagorancin ƙasa (National Leadership Council), Northern Christian Professionals ta shiga ƙawancen Arewa Democratic Stakeholders Forum a hukumance, tare da bayyana goyon bayanta ga Gangamin Fafutukar Shigar Matasan Arewa Cikin Mulki, wanda Comrade Haruna Sardauna ke jagoranta.

Ƙawancen ya ƙunshi ƙungiyoyin goyon bayan siyasa sama da 329, ƙungiyoyin addini da na farar hula, wadanda suka haɗa kai domin bayyana buƙatu da damuwar al’ummar Arewa kan shugabanci, siyasa da tafiyar da harkokin ƙasa.

A cewar ƙungiyar, haɗin gwiwar zai samar da wata dama ta bai wa ɓangarori daban-daban damar yin aiki tare wajen neman hanyoyin da za su taimaka wajen biyan buƙatun yankin Arewa da kuma ƙarfafa dimokuraɗiyyar Nijeriya.

Mai Gudanarwa na ƙasa na Northern Christian Professionals, Hon. Izaac Abrak, ya jagoranci wani taro a Abuja da aka tattauna batutuwan da suka shafi ƙoƙarin Arewa Democratic Stakeholders Forum na tuntubar shugabannin jam’iyyar APC da kuma Fadar Shugaban ƙasa.

Abrak ya ce, dandalin ya fara tuntubar manyan masu ruwa da tsaki daga Arewa da sauran sassan ƙasar, ciki har da wasu manyan jami’an gwamnatin Shugaba Tinubu, domin isar da buƙatun magoya baya da kuma tabbatar da cewa ana sauraron muryoyinsu.

Ya kuma jaddada cewa, duk da ce-ce-ku-cen da suka dabaibaye tsarin takarar Musulmi da Musulmi a zaɓen 2023, Northern Christian Professionals ta ci gaba da goyon bayan tikitin Tinubu-Shettima, tana mai cewa manufarta ita ce nasarar jam’iyyar APC baki ɗaya ba tare da neman wata fa’ida ta ƙashin kai ba.

Yayin da yake sake tabbatar da biyayyarsu ga APC, Abrak ya ce lokaci ya yi da ya kamata a duba irin gudunmawar da magoya bayan jam’iyyar suka bayar tare da samar musu da damar shiga cikin tsarin shugabanci da harkokin siyasa.

Ya yi kira ga Fadar Shugaban ƙasa da shugabannin APC da su saurari buƙatun masu ruwa da tsaki, musamman matasa, domin tabbatar da cewa waɗanda suka taka rawa wajen gina jam’iyyar da tallafa mata suna samun damar taka muhimmiyar rawa a tsarin mulki.

Haka kuma, Abrak ya buƙaci shugabannin ƙungiyoyin da ke goyon bayan APC a faɗin Arewa da su shiga ƙawancen, yana mai cewa haɗin kai zai ƙara ƙarfafa matsin lamba da tattaunawa kan shigar matasa cikin harkokin siyasa da shugabanci.

Bayan wani taro da aka gudanar kwanan nan da Ministan Bunƙasa Matasa, Abrak ya ce ya fi dacewa a yi amfani da tattaunawa wajen warware matsaloli a cikin jam’iyya maimakon rikici ko arangama, musamman yayin da zaɓen 2027 ke ƙaratowa.

Domin ƙara ƙarfafa haɗin gwiwar, Abrak ya kafa kwamiti mai mambobi biyar, wanda zai gana da Shugaban Arewa Democratic Stakeholders Forum, Hon. Haruna Sardauna, domin gabatar da yarjejeniyar haɗin gwiwa da kuma tabbatar da goyon bayan Northern Christian Professionals ga Gangamin Fafutukar Shigar Matasan Arewa Cikin Mulki.

ƙungiyar ta ce manufarta ita ce ganin an ƙara ba matasan Arewa damar shiga harkokin mulki da yanke shawarar da ta shafi makomar yankin, tare da ci gaba da goyon bayan sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027.

Northern Christian Professionals ta bayyana fatan cewa ci gaba da tattaunawa da kuma haɗa kan masu ruwa da tsaki a ƙarƙashin dandali guda zai taimaka wajen buɗe ƙarin damammaki ga matasan Arewa, tare da ƙara musu damar taka rawar gani a siyasar ƙasa a lokacin da zaɓen 2027 ke ƙaratowa.

By ukarofi

Leave a Reply