INEC ta tabbatar da Dakta Nafi’u Sankara a matsayin ɗan takarar sanatan Kano ta Tsakiya a PDP

Spread the love

Jam’iyyar PDP Reshen Jihar Kano, ta sanar da cewa Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta tabbatar da sunan Dakta Nafi’u Sankara a matsayin ɗan takarar da jam’iyyar ta tsayar na kujerar sanata mai wakiltar Mazaɓar Kano ta Tsakiya.

A sanarwar da Sakataren yaɗa labaranta ya fitar a ranar Asabar, ya ce an sunansa cikin jerin sunayen ’yan takara na ƙarshe da INEC ta wallafa a hukumance, wanda hakan ya sake tabbatar da matsayinsa a matsayin ɗan takarar Jam’iyyar PDP na Kano ta Tsakiya a zaɓen da ke tafe.

Reshen Jam’iyyar PDP na Jihar Kano na maraba da wannan tabbaci na hukuma, tare da kira ga dukkan ’yan jam’iyya, magoya baya da masu ruwa da tsaki a Kano ta Tsakiya da su ci gaba da kasancewa cikin haɗin kai, zaman lafiya da jajircewa wajen ganin nasarar Jam’iyyar PDP.

“Muna da yakinin cewa ta hanyar haɗin kai, jajircewa da ƙoƙarin kowa da kowa, Jam’iyyar PDP za ta ci gaba da samar da ingantacciyar wakilci mai nagarta ga al’ummar Kano ta Tsakiya”, inji Sakataren jam’iyyar

Saboda haka, jam’iyyar na kira ga dukkan mambobi da magoya bayanta da su yi watsi da duk wani saƙo ko bayanin da ya saɓa wa wannan tabbaci na INEC dangane da takarar Dr. Nafi’u Sankara, su kuma ci gaba da mai da hankali wajen shirye-shiryen kamfen da manufofin jam’iyyar na zaɓe.

By Babaji

Leave a Reply