Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Tsohon Sufeto-Janar na ’yan sandan Nijeriya, Mohammed Adamu, ya ce zai bai wa fannin samar da abinci da bunƙasa noma muhimmanci idan aka zaɓe shi a matsayin gwamnan Jihar Nasarawa a zaɓen 2027.
Adamu, wanda ke takarar gwamna a ƙarƙashin jam’iyyar Social Democratic Party (SDP), ya bayyana hakan ne ranar Talata yayin wani shirin tallafa wa manoma a yankin Nasarawa ta Arewa.
Ya ce shirin na da nufin tallafa wa manoma da kayan aiki da sauran abubuwan da za su taimaka wajen ƙara yawan amfanin gona da bunƙasa harkar noma a yankin.
Tsohon IGP ɗin ya bayyana cewa gwamnatinsa za ta sanya noma da samar da abinci a sahun gaba cikin manufofinta na ci gaban jihar.
Ya ce: “Dole ne mu bai wa manomanmu kayan aikin da suke buƙata domin su ƙara yawan abin da suke samarwa. Tsaron abinci zai kasance cikin abubuwan da gwamnatina za ta ba fifiko.”
A cewarsa, samar wa manoma ingantattun kayan aiki ba kawai zai ƙara yawan abinci ba, har ila yau zai sa harkar noma ta zama abin sha’awa tare da rage wahalar da manoma ke fuskanta wajen amfani da hanyoyin noma na gargajiya.
