Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Tsohon Gwamnan Kano kuma jagoran Kwankwasiyya, Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi Alla-wadai da harin da aka kai wa tawagar ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC, Peter Obi, yayin da yake kan hanyarsa zuwa Jihar Benue.
Sanata Kwankwaso ya bayyana hakan ne a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook ranar Talata.
Kwankwaso ya ce daƙilewa da kai wa ayarin Obi hari domin hana shi shiga Makurdi wani mummunan lamari ne ga dimokuradiyyar Nijeriya.
Ya buƙaci Gwamnatin Jihar Benue ta gaggauta gano tare da gurfanar da waɗanda ke da hannu a lamarin, tare da tabbatar da tsaron Obi da tawagarsa.
Kwankwaso ya kuma yi kira ga Shugaba Bola Tinubu da ya gargaɗi gwamnonin jihohi, musamman na APC, kan duk wani mataki da ka iya yin barazana ga dimokuraɗiyya.
Ya kuma buƙaci ƙasashen duniya da ƙungiyoyin sa ido kan zaɓe su lura da lamarin tare da matsa wa hukumomin Nijeriya lamba su kare ‘yancin ‘yan siyasa da kuma tabbatar da bin doka.
