Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Shugaban Jam’iyyar APC na ƙasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya fara hutun makonni biyu a ƙasar waje, domin samun damar hutawa da kuma tsara dabarun da za a tunkari babban zaɓen 2027.
A wata sanarwa da mai ba shi shawara kan yaɗa labarai, Abimbola Tooki, ya fitar, an ce Yilwatda ya shafe shekara ta farko a kan mulki yana gudanar da tafiye-tafiye, shawarwari da taruka domin ƙarfafa da sake fasalin jam’iyyar.
Sanarwar ta ce daga cikin nasarorin da aka samu ƙarƙashin jagorancinsa akwai gudanar da babban taron jam’iyyar na ƙasa, ƙarfafa rassan APC da gudanar da zaɓen fidda gwani a matakai daban-daban.
An bayyana hutun a matsayin damar da shugaban APC zai yi amfani da ita wajen farfaɗo da ƙarfi da kuma nazarin manyan nauyin da ke gabansa yayin da jam’iyyar ke shirin zaɓen 2027.
Yilwatda zai kuma yi amfani da lokacin wajen kammala shirye-shiryen taron kwamitin gudanarwa na ƙasa (NWC), wanda zai duba ci gaban jam’iyyar da ƙalubalen da ke gabanta.
APC ta ce rashin shugaban jam’iyyar ba zai kawo cikas ga ayyukanta ba, domin NWC zai ci gaba dad gudanar da harkokin jam’iyyar bisa kundinta. Ana sa ran Yilwatda zai dawo Nijeriya bayan hutun makonni biyun.
