Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Karamar Ministar Abuja, Mariya Mahmud, ta bayyana cewa jam’iyyar APC za ta ci gaba da mulkin Nijeriya bayan shekarar 2031.
Mahmud ta bayyana haka ne yayin kaddamar da kungiyar City Boy Moɓement (CBM) a Kano, inda ta ce babu wani gurbi a fadar shugaban kasa har zuwa shekarar 2031, tana mai goyon bayan sake zaben Shugaba Bola Tinubu.
Ta ce matasa da mata na da muhimmiyar rawa wajen samun nasarar APC, saboda matasa sun kunshi kaso mai yawa na al’ummar Nijeriya.
Ministar ta kuma yi nuni da wasu manufofin gwamnatin Tinubu, ciki har da shirin rancen karatu na NELFUND, tana cewa nasarorin gwamnatin za su taimaka wajen neman kuri’u a babban zaben kasa.
Daraktan-Janar na CBM, Francis Oluwatosin Shoga, ya ce kungiyar na da burin samun mambobi miliyan 10 a fadin Nijeriya, domin karfafa tsarin siyasar jam’iyyar tun daga tushe.
A Kano kuwa, mai kula da CBM na jihar, Nasir Bala Ja’oji, ya bayyana cewa kungiyar ta riga ta yi wa mutane 189,111 rajista a jihar, inda ya bukaci kara karfafa tsarin shugabanci da hada kan magoya baya a ƙananan hukumomi.
