
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Tsohon Babban Hafsan Tsaron Shugaban mulkin soji, Janar Sani Abacha, Manjo Hamza Al-Mustaph (mai ritaya), ya yi watsi da kalaman wani tsohon jami’in Hukumar Tsaro ta Farin kaya (DSS) akan lokutan ƙarshe na marigayin shugaban.
Al-Mustaph ya bayyana kalaman a matsayin ƙarya, inda ya kuma yi kira ga ‘yan Nijeriya da su watsi da su.
Tsohon babban hafsan ya faɗi haka ne a wata hira da manema labarai bayan taron tunawa da marigayi Janar Hassan Usman Katsina karo na uku da aka gudanar Arewa House da ke Jihar Kaduna a ranar Asabar.
Ya yi tsokacin ne bayan tsohon jami’in na DSS ya furta kalaman akan abin da ya sani game da mutuwar Abacha a ranar 8 ga Yunin 1998 a wata hira.
“Wasu ne suka umarci yaron ya faɗi waɗannan ƙarairayin. Ina da ɗaukar CCTV na abin da ya faru a wajena, don haka abin da ya faɗa ba gaskiya ba ne,” inji Al-Mustaph.
A cewarsa, yana da hujjar da ke cin karo da abin da jami’in ya faɗa akan al’amarin, saidai bai bayar da ƙarin bayani akan ɗaukar ba ko yana da manufar yaɗa ta ga al’umma.
Akan haka ne ya yi kira ga ‘yan Nijeriya da su yi watsi da iƙirarin, yana mai cewa ba daidai ba ne yin ire-iren waɗannan zarge-zargen akan mamacin da ba zai iya kare kansa ba.
Abacha ya rasu ne a Abuja bayan shafe shekaru sama da huɗu yana mulkin Nijeriya, inda Gwamnatin Tarayya ta ce ya rasu ne sakamakon fama da wani rashin lafiya na ɗan lokaci, amma ainihin abin da ya sabbaba mutuwarsa ya zama ɗaya daga cikin ababe masu sarƙaƙiyar bayani a tarihin siyasar Nijeriya.
