Gwamnatin Katsina ta gudanar da jarrabawa ga mahaddatan Alƙur’ani

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamnatin Jihar Katsina ta shirya gudanar da jarrabawa ga mahaddatan Alƙur’ani mai girma a faɗin jihar Katsina domin ɗaukar nauyin karatun su a ɓangaren aikin likita da sauran ɓangarorin kiwon lafiya.

An gudanar da jarrabawar a ɗakunan jarrabawa da ke jami’ar Umaru Musa Yar’adua nan cikin garin Katsina.

Shirin wanda ofishin mai bawa gwamna shawara na musamman a kan karatun Alkur’ani da yaran da ba su zuwa makaranta, Hon Injiniya Tasi’u Dahiru Dandagoro ke gudanarwa.

Da yake gabatar da jawabin sa Hon. Tasiu Ɗandagoro ya bayyana cewa” wannan shiri gwamnatin jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin Malam Dikko Umar Raɗɗa ta zo da shi kuma za ta gudanar da shi a karon farko.

Hon. Ɗandagoro ya yi dogon jawabi na irin tsarin da aka yi domin tabbatar da anyi shiri cikin tsari da kuma gaskiya da riƙon amana kamar yadda mai girma gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umar Raɗɗa ya bada umarni.

A nasa jawabin babban mai taimaka ma gwamnan jihar Katsina akan harkokin addinai Mal. Ismail Abdullahi Matazu ya bayyana irin tsare tsaren da aka yi domin gudanar da wannan jarabawa.

A nasa jawabin wakilin ƙungiyoyin al’umma Dr. Bashir Usman Ruwangodiya ya yabama ƙoƙarin gwamnatin jihar Katsina na samar da wannan shiri tare da kira ga alkalan da za su jagoranci jarabawar da su ji tsoron Allah.

Malamai da dama ne daga shiyyoyi uku na jihar Katsina suka gabatar da jawabai tare da nasihohi a wurin gudanar da jarrabawar.

Taron jarrabawar ya samu halartar masu taimaka ma gwamnan jihar Katsina a kan harkokin ɗarika da izala, wakilan ma’aikatu, hukumomin gwamnati da dai sauran su.

By ukarofi

Leave a Reply