‘Yan-bindiga sun kai hare-hare a sassan Neja

Daga jaridar Manhaja

‘Yan-bindiga sun kai hare-hare a wasu kauyukan karamar hukumar Paikoro da ke Jihar Neja, inda suka hallaka mutum shida tare da yin garkuwa da mutum biyar sannan suka jikkata sama da mutum 20.

Bayanai daga jihar sun nuna ‘yan-bindigar sun soma ta’addacinsu ne daga Asabar da ta gabata zuwa washegari Lahadi da rana.

Wani mazaunin daya daga cikin kauyukan da harin ya shafa mai suna Abubakar Azaido, ya shaida wa Manhaja ta tarho cewa sama da mutum 20 da suka jikkata a harin aka kai babbar asibitin Kafin Koro. Ya ce, akalla mutum 3000 ne suka tsere suka bar gidajensu don neman mafaka a wasu wurare.

“‘Yan-bindigar suna da yawa, sun haura 200 kuma a kan babura suka kai wa kauyukan hari. Sun wawushe wani shagon sayar da kayayyakin babura a kauyen Amale”, inji Azaido.

Ya ce, yayin harin an kashe mutum 4 a kauyen Gwajau, haka ma a kauyen Amale an hallaka mutum 2, sannan sun sace mutum hudu a Dakolo gami da wani fasto a kauyen Nani.

Kauyukan da hare-haren suka shafa sun hada da; Amale da Beni da Barakwai da Kakuri da Gudani da Abolo da Nani da Gwajau da Kubi, Zakolo da Kado da kuma Dakolo, kamar yadda Azaido ya shaida wa Manhaja.

Binciken Manjaha ya gano shanu sama da 200 ne ‘yan-bindigar suka yi awon gaba da su inda suka doshi iyakar Neja da jihar Kaduna.

Ya zuwa hada wannan labari, duk kokarin da aka yi don jin ta bakin Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan jihar Neja ASP Abiodun Wasiu, hakan ya ci tura.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *