Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Matatar Mai ta Dangote ta jefa harkokin kasuwar man fetur ta ƙasa cikin sabon yanayi na rashin tabbas bayan da ta fara amfani da tsarin sayar da fetur da farashinsa ke dogara da dalar Amurka. Matakin ya sa dillalan man fetur da dama suka dakatar da sayen kaya, lamarin da ke ƙara tayar da fargabar yiwuwar tangardar samar da fetur a sassan ƙasar.
Dillalan man fetur sun shaida cewa ayyukan ɗaukar fetur daga matatar sun ragu matuƙa, yayin da yawancin masu kasuwanci suka dakatar da sayayya mai yawa suna jiran a fayyace sabon tsarin farashin da kuma yadda zai shafi farashin man da ake shigowa da shi daga ƙasashen waje. Sun bayyana cewa sabon tsarin na iya sa farashin fetur a cikin gida ya riƙa sauyawa gwargwadon tashin ko faɗuwar darajar dala, abin da ka iya ƙara wa masu amfani da mai nauyin rayuwa.
Sai dai duk da wasu dillalai sun yi zargin cewa Matatar Dangote da ke Lekki ta dakatar da loda manyan motocin dakon mai gaba ɗaya, jami’an Kamfanin Dangote sun musanta wannan iƙirari, suna cewa ana ci gaba da gudanar da ayyuka kamar yadda aka saba.
Duk da wannan musantawa, dillalan man fetur sun ce rashin tabbas kan sabon tsarin farashin ya tilasta musu yin taka-tsantsan, saboda suna tsoron sayen fetur a farashin yanzu, daga baya kuma farashin ya sauko su tafka asara.
Sakataren Yaɗa Labarai na ƙungiyar Masu Dillancin Man Fetur Masu Zaman Kansu ta Nijeriya (IPMAN), Chinedu Ukadike, ya ce dillalai na fuskantar yanayin kasuwa mai wahalar hasashe. Ya ce, fetur da ake sayarwa yanzu shi ne wanda aka adana a tankokin ajiya, wanda aka saya tsakanin Naira 1,250 zuwa Naira 1,300 kan kowace lita.
A cewarsa, rashin tabbas kan sabon ɗanyen mai da za a tace da kuma farashin sabon man da aka shigo da shi daga ƙasashen waje ne ya ƙara rikita kasuwar. Ukadike ya ce, masu kasuwanci ba su san ko bayan sun ɗauki kaya farashin zai ƙaru ko kuma zai ragu ba, alhali masu amfani da mai suna sa ran a ci gaba da sayar musu da shi a farashin da ake sayarwa a lokacin. Ya bayyana cewa, ba a dakatar da rabon fetur gaba ɗaya ba, amma yawan man da ake ɗagawa daga matatun ya ragu sosai. Ya kuma yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta warware taƙaddamar tsarin farashin domin hana ƙarin rikicewa a kasuwar mai.
Rahotanni daga yankin Kudu maso Yamma sun nuna cewa wasu gidajen mai sun dakatar da sabbin sayen fetur, yayin da wasu kuma suka rufe ayyukansu na ɗan lokaci saboda rashin tabbas da ke tattare da sabon tsarin.
Shugaban shiyyar Kudu maso Yamma na IPMAN, Oyewole Akanni, ya tabbatar da hakan, yana mai cewa matsalar ta samo asali ne bayan dakatar da loda man fetur daga Matatar Dangote kimanin kwanaki huɗu da suka gabata.
Ya ce hakan ya sa dillalai suka koma sayen fetur daga ma’ajiyun masu zaman kansu, inda farashi ya yi tashin gwauron zabo. A cewarsa, mafi ƙarancin farashin fetur daga ma’ajiyar Legas yanzu yana tsakanin Naira 1,200 zuwa Naira 1,220 kan kowace lita, ba tare da kuɗin sufuri ba. Har ila yau, ya soki Matatar Dangote bisa rashin sanar da dillalai tun kafin dakatar da sayar da mai ko bayyana dalilin hakan.
Sai dai wani jami’in Kamfanin Dangote ya bayyana cewa rahotannin da ke cewa matatar ta dakatar da loda fetur ba gaskiya ba ne. Ya ce, duk wanda yake son tabbatarwa zai iya zuwa matatar ya gani da idonsa cewa ana ci gaba da loda fetur. Jami’in ya kuma yi zargin cewa wasu masu shigo da fetur daga ƙasashen waje na fuskantar matsin lamba saboda tashin farashin fetur a birnin Lome na ƙasar Togo.
A halin yanzu tattaunawar da ke gudana tsakanin Gwamnatin Tarayya da Matatar Dangote kan sabon tsarin sayar da fetur da dala ba ta kai ga cimma matsaya ba.
Wani babban jami’in gwamnati ya bayyana cewa taƙaddamar ba ta tsaya kan farashi kaɗai ba, har ma ta shafi yadda ake samar wa matatar ɗanyen mai da kuma ci gaba da bai wa wasu kamfanoni lasisin shigo da fetur. A cewarsa, Matatar Dangote na ganin babu dalilin ci gaba da bayar da lasisin shigo da fetur alhali tana da ƙarfin tace isasshen mai.
